1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaitaccen tarihin Marie-Louise Eta

Da Silva, Michael ZMA
November 30, 2023

A karon farko a tarihin wasannain kwallon kafa na Bundesliga a tarayyar Jamus, an samu mace a matsayin mai horar da 'yan wasa a kungiyar kwallon kafa ta Union Berlin.

https://p.dw.com/p/4ZcVD
Deutschland Marie-Louise Eta ist Co-Trainerin der U 19 bei Eisern Union
Hoto: Sabine Gudath/IMAGO

 An haifi Marie-Louise Eta a birnin Dresden a shekarar 1991, inda ta zama mai horar da 'yan wasa a shekaru 26 bayan ta ajiye nata takalman buga kwallon. Ta fara aiki ne a kungiyar kwallon kafa ta Jamus, inda ta kula da kungiyoyin mata masu buga kwallon kafa wa kasa kuma ke taka leda a matakin kasa da kasa, kafin ta yi wannan sauyin alkiblar zuwa horar da maza. A taburin na Bundesliga dai kungiyar ta Union Berlin na can kasa, tawagar da ta jima ba tare da wani takamammen jagoran horar da wasa ba, kuma har yanzu ke laluben damar lashe gasarta ta farko tun daga watan Augusta. Bayan korar Urs Fischer, kocin da ya jagoranci tawagar ta Union Berlin a karon farko na tarihinta zuwa gasar Bundesliga, kafin jagorantar 'yan wasan zuwa gasar zakarun Turai, shugabn kungiyar ta Union Berlin Dirk Zingler ya ayyana cewar, an samo wadda  ta fi dacewa da yin aikin.

Marie-Louise Eta tshohuwar 'yar kwallon kafa ta zama ta farko mai horar da maza a Jamus

Marie Louise Eta
Marie Louise EtaHoto: Andreas Gora/dpa/picture alliance

 Bayan Eta, babu mata da yawa da za su iya cewa sun horar da maza da mata da kwarewarsu. Daya daga cikin wadanda aka zaba ita ce Imke Wübbenhorst, wacce a halin yanzu ita ce shugabar kungiyar Young boys, reshen mata a Switzerland. Ita ma tsohuwar abokiyar wasan Eta ce a BV Cloppenburg na tsawon kakar wasanni biyu. Wübbenhorst ta ce "Eh, ban yi mamakin haka ba domin ina ganin sun zabe ta a matsayin mataimakiyar mai horar da tawagar matasa mafi girma da suke da ita a kungiyar, kuma shi ya sa suka gamsu da halayenta".Matan biyu sun buga kakar wasa tare a mataki na biyu da kuma wata kakar, a gasar Bundesliga ta mata bayan  sun yi nasara.A wata hira da DW, Wübbenhorst ta bayyana yadda sukan tattauna dabarun wasan kwallon kafa da ma aiwatar da sauye-sauyen dabaru a fagen wasa a lokacin wasanni.

Tana fatan ganin ta farfado da tagomashi na kulob din Union Berlin

Marie Louise Eta
Marie Louise EtaHoto: Rauch/nordphoto/picture alliance

Ta ce" Ina fatan cewa matakin zai yi aiki kuma su sami nasara kuma ba wanda zai ce saboda mataimakiyar kocin mace ce. Domin fadin hakan a wurina wauta ne. Muna bukatar wanda ya zo kan wannan matsayi kuma ya nuna cewar da gaske yake. Bangaren al’umma ke'nan, amma mahukuntan manyan kungiyoyin kwallon kafa suna la'akari ne da cancantar aiki da tasirin mai yin sa". Wübbenhorst ta ce nutsuwar tsohuwar abokiyar wasarta da hazaka shi ne abin da ya bambanta ta da sauran sao'inta, kuma ta yi imanin cewa sabon matsayinta na mataimakiyar koci a kungiyar ta  Union Berlin ya dace da kwarewarta. Eta ta jawo hankali ba kawai don kwarewarta a fannin horarwa ba amma amma har da jinsinta na kasancewa mace. Masu sharhi kan harkokin motsa jiki dai na ganin cewar, yakamata nadin Eta ya bude kofa ga mata da yawa su bi sawu kamar a Amurka, inda aka dade ana bai wa mata matsayin mataimakan masu horar da kungiyoyin wasanni na maza, kasancewar har yanzu a Turai ana jan kafa  wajen tabbatar da hakan.