1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniJamus

Labarin Wasanni: 30.10.2023

Mouhamadou Awal Balarabe AMA
October 30, 2023

Kungiyar Sprinboks ta Afirka ta Kudu ta kafa tarihi a fannin zari-ruga, a yayin da dan damben Kamaru Francis Nganou na shan yabo game da rawar da ya taka a karawa da ya yi da Tyson Fury na Ingila.

https://p.dw.com/p/4YCCm
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da tawagar 'yan wasan Rugby na murnar lashe kofin duniya
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da tawagar 'yan wasan Rugby na murnar lashe kofin duniyaHoto: Thibault Camus/AP Photo/picture alliance

Afirka ta Kudu ta lashe gasar cin kofin duniya ta zari ruga a karo na hudu (4) a tarihinta bayan da ta samu nasara a kan New Zealand  da ci 12-11 a wasan karshe da ya gudana a Stade de France na kasar Faransa.

Wannan tawaga da ake wa lakabi da Springboks ta yi tazarce ne domin ita ce ke rike kambun zakaran duniya tun a shekarar 2019, hasali ma dai, Afirka ta Kudu ta zama tawaga daya tilo da ta lashe gasar cin kofin duniya a gaban All Black na New Zeland sau biyu, kana dadin dadawa ma Springboks ba ta taba shan kashi a wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta Rugby ba.

'Yan Afirka ta Kudu sun shafe karshen mako suna murnar bajintar da kasarsu ta nuna, kasancewa ta zama kasa da ta fi yawan lashe kofin zari ruga a duniya. Godiya ta tabbata ga kyaftin Sprinboks Siya Kolisi wanda ya fi shan yabo da godiya sakamakon rawar da ya taka wajen hada kan 'yan wasa tare da sanya al'ummar Afirka ta Kudu cikin farin ciki.

Kungiyar Springbok bata taba samun irin wannan karbuwa a cikin gida ba musamman saboda surka kalolin fatan 'yan wasan da aka yi, baya ga yanayin tattalin arziki da zamantakewa mai sarkakiya da kasar ke fuskanta tun bayan bullar annobar Covid-19, 'yan kasar da dama ne suka fantsama kan tituna don nuna farin cikinsu ciki har da wannan dan kasar da ke cewa "Abin mamaki. Ban san ma abin da zan ce ba. Na yi tsammanin za mu baras da wannan wasan, amma ratar maki daya ya ba mu nasara kuma ina murna sosai. Ita wannan kungiyar, tana da wani abu na musamman. Sun hada kan al'umma. Duba, duba, abu ne mai kyau".

Dan damben Kamaru Francis Nganou na shan yabo

Dan damben Kamaru Ngannou da abokin karawarsa Tyson Fury
Dan damben Kamaru Ngannou da abokin karawarsa Tyson Fury Hoto: Yazeed Aldhawaihi/AP/picture alliance

Francis Ngannou da ya yi fice a fannin MMA a baya ya kutsa kai a karon farko a damben Ingila a wasan da ya gudana a karshen makon a Ryad na kasar Saudiyya. Sai dai tauraron damben na kasar Kamaru ya fara da kafar hagu a lokacin da ya tinkari zakaran duniya na ajin masu nauyi Tyson Fury, amma duk masu bibiyar boxing sun yi iftifakin cewar ya burge matuka gaya.

Hasali ma dai, yayin da masu lura da al'amuran wasanni da dama ke sa ran za a mamaye dan Kamarun, amma Francis Ngannou ya wa dan Biritaniya girgizar da bai taba yin irinsa ba ta hanyar kayar da shi a zagaye na uku.

Duk da cewa Tyson Fury ya fi shi da maki daya, a hukunci mai cike da cece-kuce da alkalan wasa suk yanke, dan wasan na Kamaru ya ce ya gamsu da kwazonsa a wannan damben. sai dai 'yan wasa daban-daban na Boxing irin su Doumbe da ma 'yan kwallon kafa na ganin cewar, an yi wa Nganou kwange.

Su ma dai 'yan kasarsa ta kamaru da suka shafe dare wajen kallon damben sun nuna bakin cikinsu kasancewar sakamakon ya saba wa fatan su na samun nasara, lamarinn da ya sa suka shafe karshen mako suna bakin ciki.

Gasar gasar Superleague ta yi armashi

 A fannin kwallon kafa, a karshen makon nan ne aka gudanar da wasan kusa da na karshe na gasar Superleague ta nahiyar Afirka, wanda kungiyoyin da ke wasa a gida ne suka yi nasara.

Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu da ke daukar nauyin wasan ta doke Al Ahly ta Masar da  1-0 inda dan wasan da ke buga wa Bafana Bafana Thapelo Maseko, ya zura kwallo daya tilo a wasan. Wydad Casablanca ta kasar Maroko ta yi nasara ita ma da ci daya mai ban haushi sakamakon kwallon da Hicham Boussefiane ya ci mai tsaron gida na kungiyar Esperance de Tunis ta Tunsiya.

A ranar Laraba mai zuwa ne ne za a yi zagaye na biyu na wasannin na kusa da na karshe.

Bayern Munich ta yi Darmstadt dukar fitan arziki

'Yan wasan FC Bayern München da takwarorinus na Darmstadt 98
'Yan wasan FC Bayern München da takwarorinus na Darmstadt 98Hoto: Tom Weller/dpa/picture alliance

A fagen babban lig din kwallon kafar Jamus "Bundesliga" inda aka gudanar da wasannin mako na tara a karshen mako kuwa, Bayern Munich ta nuna wa Darmstadt cewar ruwa ba sa'ar kwando ba ne saboda ta yi mata dukan kawo wuka da ci 8-0.

Sai dai wasan ya zo da akasi saboda alkalin wasa ya bayar da jan kati uku, daya ga Bayern da biyu ga Darmstadt tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma bai hana Leroy Sané da Jamal Musiala kowanne zura kwallaye biyu a ragar Darmstadt ba, yayin da zakakurin dan wasan gaba na Bayern munich Harry Kane ya zura kwallaye uku.

Yanzu dai Harry Kane yana kara kusantar Serhou Guirassy na Stuttgart a jerin 'yan wasan da suka zura kwallaye, inda dan wasan na Guinea wanda a halin yanzu yake fama da rauni ya fi shi da kwallaye biyu, kuma duk ruwan kwallaye da Bayern Munich ta yi wa Damrstadt ba ta dare saman teburin Bundesliga ba, inda take a matsayi na biyu da maki 23.

Ita kuwa Bayer Leverkusen ta ci gaba da jan zarenta ba tare da ya tsinke mata ba. 'Yan wasan koci Xabi Alonso sukn samu nasarar su ta takwas 8 a wasanni tara inda suka doke Friborg da ci 2-1, lamarin da ya ba su damar jagorantar Bundesliga da maki 25.

Sai dai Yaya-karama Borussia Dortmund ba ta yi abin yabo ko fallasa ba saboda ta tashi 3-3 da Frankfurt, a daidai lokacin da ya rage mako guda ta yi daya daga wasa mafi tsauri a kakar wasan da Bayern Munich a Signal Iduna Park. Amma dai Dortmund za ta ci gaba da zama a matsayi na 4 a kan teburi, kuma yanzu maki hudu ne ke nisanta ta da Leverkusen da kuma ratar maki biyu da Bayern.

A sauran wasanni kuwa, Augsburg ta yi nasarar doke Wolfsburg da ci 3-2, yayin da RB Leipzig ta lallasa Fc Köln da ci 6-0. Ita kuwa Monchengldbach ta mamaye Heideinheim da ci 2-1, yayin da Werder Bremen ta samu nasara  a kan Union Berlin da 2-0. A Nata bangaren Stutgart ta yi rashin sa'a a karawa da ta yi da Hoffenheim inda aka tashi ci 2-3, yayain da aka tashi 2-2 tsakanin Bocum da Mainz.

Sauran manyan wasannin Lig na kasashen Turai

Dan wasan kwallon kafa Fabio Grosso
Dan wasan kwallon kafa Fabio GrossoHoto: picture-alliance/dpa

A Ligue 1 na kasar Faransa kuwa, an dage wasa tsakanin Marseille da Lyon bayan jifan motar da ke dauke da 'yan wasa OL inda koci Fabio Grosso ya samu rauni yayin da tagogin motar suka farfashe a gabanin wasannin mako na 10. Shugabannin hukuma da kungiyoyin kwallon kafa na Faransa sun nuna kaduwa bayan wannan mummunan harin da ke neman zama ruwan dare a kasar.

Ministar wasanni Amélie Oudéa-Castéra ta danganta abin da ya faru da ayyuka da gwamnatinsu ba za a amince da su ba saboda suna rage kimar kwallon kafa da ma sauran wasanni wasanni, saboda haka ne ta yi fatan a gudanar da bincike cikin gaggawa domin a gano wadanda suka aikata wannan aika-aika, kuma a yanke musu hukunci su mai tsanani.

Manchester City ta yi tattaki zuwa Old Trafford

A Premier Leauge kuwa, Manchester City ta yi tattaki zuwa Old Trafford kuma ta yi wa Manchester United dukan fin karfi ci 3-0, godiya ga Erling Haaland da ya zura biyu daga cikin kwallayen kuma ya taimaka ana uku, lamarin da ya ba wa kungiyar damar rike matsayinta na uku a kan teburi da maki 24.

'Yan wasan kwallon kafa na  Manchester Utd
'Yan wasan kwallon kafa na Manchester UtdHoto: Dave Thompson/AP Photo/picture alliance

A yanzu dai Liverpool ke a matsayi na biyu bayan da laya ta yi mata kyaun rufi ta hanyar doke Nottingham da ci 3-0, kwanaki kalilan bayan doke Toulouse da ci 5-1 a gasar cin kofin Europa.

Ita kuwa Tottenham ta yi nasara a kan Crystal Palace 2-1 lamarin da ya bata damar zama a saman teburin Premier League de maki 26  kuma ta kara kaimi a saman gasar a mako na 10 na gasar.

A Spain, Atletico Madrid ta yi nasara ta shida a jere a gasar a gaban sabon shiga Alaves da ci 2 a mako na 11na gasar La Liga, inda ta wuce FC Barcelona tare da darewa a matsayi na uku. Dama Barça ta baras da wasa da ta yi da abokiyar hamayyarta ta fil azal Real Madrid da ci 1-2, lamarin da ya ba wa Real Madrid ci gaba da zama jagora.