1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Labarin Wasanni: DFB ta kori Hansi Flick

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
September 11, 2023

Jamus ta yi abin kai a gasar kwallon kwando ta duniya inda ta lashe kofinta na farko, yayin da a daya hannun ta sallami mai horas da 'yan wasan kwallon kafarta sakamakon rashin tabuka abin kirki.

https://p.dw.com/p/4WDDs
BdTD | Philippines | Manila | Jamus | Nasara | Kwallon Kwando | Sabiya
Jamus ta lashe gasar kwallon kwando ta duniya a karon farkoHoto: Jayne Russell/Imago Images

Jamus ta zama zakaran kwallon kwando na duniya sakamakon nasara da maki 83 da 77 da ta samu, a fafatawarta yi da Sabiya a wasan karshe da ya gudana a birnin Manila na kasar Philippines. Wannan dai shi ne karo na biyar a jere da Sabiya ta baras da damarta a gasar cin kofin kwallon kwando ta duniya, yayin da irin wannan bajintar ke zama farau ga Mannschaft ta Jamus karkashin tauraronta Dennis Schröder wanda ya danganta lamarin da irin kokarin da suka yi na hada karfi da karfe. Schröder ne dai ya zama dan wasa da ya fi nuna bajinta a gasar cin kofin kwallon kwando ta duniya sakamakon cin maki 28 a wannan wasan na karshe, lamarin da ya ba shi damar gadar dan kasar Spaniya Ricky Rubio a wannan matsayi. A wasan neman matsayi na uku a gasar kuwa, Kanada ta doke Amurka da ke rike da kambun da maki 127 da 118.

Jamus | DFB | Hansi Flick
Korarren mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Jamus Hansi FlickHoto: Pressefoto Baumann/imago images

A fannin kwallon kafa kuwa Jamus din ta kori Hansi Flick da ke horas da babbar kungiyarta, kwana daya bayan da ta sha kashi tamkar kurar roko kuma a gida a hannun Japan da ci daya da hudu a yammacin ranar Asabar. Sai dai watanni tara kafin gasar kwallon kafa ta nahiyar Turai da za ta karbi bakunci, Jamus ta yi alkawarin ci gaba da tankade da rairaya domin kwalliyarta ta biya kudin sabulu. Tuni ma dai  jaridar Bild ta ruwaito cewar, mai horas da 'yan wasa da ke tashe kuma mai karancin shekaru, wato Julian Nagelsmann ne zai iya maye gurbin Flick da ya shafe shekaru biyu a mukamin babban mai horas da Mannschaft din ba tare da cimma wata nasara ba. Amma a halin yanzu hukumar kwallon kafar Jamus ta nemi Rudi Völler da Hannes Wolf da Sandro Wagner su ja ragamar horo wajen fuskantar tawagar Faransa, a wasan sada zumuncin da za su fafata ranar Talatar da ke tafe a birnin Dortmund.

Najeriya | Kwallon Kafa | AFCON I Victor Osimhen
Dan wasan kwallon kafar Najeriya Victor Osimhen ya yi zarraHoto: Simone Scusa/Shengolpixs/IMAGO

A nahiyar Afirka, manyan kungoyoyin kwallon kafa suna ci gaba da gudanar da wasanni karshe na neman cancantar shigar gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar wato AfCON da za ta gudana a kasar Côte d' Ivoire a badi. Kuma kamar yadda aka yi hasashe tun da farko, babbar kungiyar kwallon kafar Najeriya ta samu tikitin shiga gasar sakamakon cin kaca shida da nema da ta yi wa Sao Tome da Principe. Godiya ta tabbata da Victor Osimhen da ya  ba da gagarumar gudunmawa ta hanyar cin kwallaye uku yayin da takwaransa Victor Boniface da ke bugawa a Bayer Leverkusen ya taimaka wa Samuel Chukuweze cin kwallo a minti 84, lamarin da ya bai wa Super Eagles kammalawa a matsayi na daya a rukunin A.

AFCON | Burkina Faso | Bertrand Traore
Dan wasan gaba na Burkina Faso Bertrand TraoreHoto: CHARLY TRIBALLEAU/AFP/Getty Images

A rukunin B kuwa, Togo ta lallasa Cape Verde da ci uku dabiyu, amma ba ta kai labari ba sakamakon dibar kashi a hannu da ta yi a wasan farko. Ita dai Cape Verde ta riga ta cancaci shiga gasar rukunin B kafin wasan karshen mako, amma ta  bai wa Burkina Faso samun matsayi na farko bayan da ta tashi canjaras babu ci a wasansu da Eswatini. Ita kuwa Gambiya ta bai wa marar da kunya, inda ta kawar da Congo Brazzaville bayan da suka tashi wasa canjaras biyu da biyu. Wannan zai bai wa Gambiya damar rubuta sabon babi a fannin kwallon kafa, kasancewar wannan shi ne karo na biyu da ta cancanci shiga gasar ta AFCON a tarihinta. A halin yanzu dai, an samu kashi 90% na kasashen da suka riga suka cancanta shiga gasar kwallon kafar Afirka ciki har da Côte d' Ivoire mai masaukin baki da Aljeriya da Tunisiya da Senegal da Burkina Faso da Equatorial Guinea da Maroko da Afirka ta Kudu da Masar da Zambiya da Nigeriya da Guinea-Bissau da Cape Verde da Mali da kuma Guinea. Sai dai kuma kallo ya koma Kamaru, inda Indomitable Lions za ta buga wasanta na warewa koko warware ta, tare da Burundi a birnin Garoua a ranar Talata. Amma hadarin da ke tattare da rashin nasara ga Kamaru a kasar da ake daukar kwallon kafa tamkar addini, ya sa hukumomin daukar matakan tsaro da na kwallon kafa domin ganin cewa an mutunta sakamakon da aka samu maimakon kona gidajen 'yan wasa da far wa iyayensu.

Faransa | Kwallon Zari-ruga | Afirka ta Kudu | Nasara
'Yan wasan kwallon zari-ruga na Afirka ta Kudu na taka rawa a FaransaHoto: Mike Jones/News Images/IMAGO

Afirka ta Kudu ta fara gasar neman cin kofin kwallon zari-ruga ta duniya da ke gudana a kasar Faransa da kafar dama, inda a wasanta na farko Springboks ta mamaye abokiyar hamayyarta Scotlanda da ci 18 da uku. Wannan dai shi ne karon farko da Afrika ta Kudu ta lashe wasanta na farko a gasar cin kofin duniya, a cikin shekaru 12 da suka gabata. A wasanninta na gaba dai Afirka ta Kudu da ke rike da kofin duniya na kwallon zari-rugar, za ta kara da Romaniya da kuma Ireland a rukuni na biyu. Sai dai a lokacin da Springboks ke halartar gasar duniya a karo na bakwai, ita kuwa Namibiya wannan shi ne karon farko da take wakiltar nahiyar Afirka a wannan gasar. Sabanin Afirka ta Kudu, Namibiya ta sha kashi a hannun Italiya da ci 52 da takwas a ranar Asabar. A sauran wasannin kuwa, Wales ta tsira da kyar a hannun Fiji da ci 32 da 26. Japan da Chili sun tashi wasa 42 da 12, yayin da Ingila da Ajantina suka tashi wasa 27 da 10.

BdTD | Amurka | New York | Novak Djokovic | Zakara | U.S. Open
Novak Djokovic ya kafa tarihi, bayan da ya lashe gasar tennis ta U.S. OpenHoto: MIKE SEGAR/REUTERS

A fagen Tennis kuwa Novak Djokovic mai shekaru 36 a duniya ya lashe gasar U.S. Open karo na hudu, bayan da ya doke Daniil Medvedev a wasan karshe da ci shida da uku da bakwkai da shida da bakwai da biyar da kuma shida da uku. Dadin dadawa ya kafa cikakken tarihi na samun kofin Grand Slam guda 24, kamar yadda 'yar kwallon tennis din Australia Margaret Court ta yi a 1973. Tuni ma dai kwana daya bayan nasarar, Djokovic ya koma saman teburi a jadawalin matsayin ATP. A yanzu dai Alcaraz shi ne na biyu, kuma Medvedev ya karfafa matsayinsa na uku a duniya a fagen tennis. A bangaren mata kuwa, zakakurar tennis din nan 'yar Amurka Coco Gauff mai shekara 19 a duniya, ta doke Aryna Sabalenka a US Open da ci biyu da shida da shida da uku da shida da biyu  tare da lashe gasar Grand Slam ta farko a tarihinta. Sai dai duk da kayen da ta sha a US Open, 'yar kasar Belarus Aryna Sabalenka ce ke jagorantar jerin sunayen WTA a karon farko, lamarin da ke zama dannar kirji a gare ta kuma ya kawo karshen mamayar da Iga Swiatek 'yar kasar Poland da ta koma matsayi na biyu ta dade tana yi. Ita kuwa 'yar Amurka Coco Gauff ta tashi daga matsayi na shida zuwa matsayi na uku, a fagen tennis a duniya.