1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Nijar ta katse nuna wasannin Turai

Mouhamadou Awal Balarabe SB/AMA
September 18, 2023

Laya ta yi wa kungiyar Afirka ta Kudu kyau rufi a gasar zari ruga ta duniya, inda ta yi Romaniya dukan kawo wuka ci 76-0. 'Yan Nijar ma'abotan kwallon kasashen Turai sun shiga halin tasku sakamakon katse kafofin wasannin

https://p.dw.com/p/4WTIH
Rugby Neuseeland - Südafrika
Hoto: Simon King/Pro Sports Images/IMAGO

Gasar neman cin kofin duniya na zari ruga na ci gaba da kankama a kasar Faransa, inda a Afirka ta Kudu ta share wa nahiyar Afirka hawaye ta hanyar cin zarafin Romaniya da ci 76-0!. Wannan yana nufin cewar abokiyar hamayyar Springboks ba ta ci kwallo ko da daya ba a tsawon wannan wasa da ke zama na biyu a jere da ta samu nasara. Hasali ma dai, baya ga jan zarenta da take yi ba tare da ya tsinke mata, Afirka ta Kudu da ke rike da kofin zari ruga na duniya ta kasance wacce ake zira mata mafi karancin kwallo a wannan gasa a halin yanzu. Sai dai za ta yi wasanta na gaba ne da fitattar kungiyar Rugby ta Ireland, wacce ke hankoron lashe kofin a bana.

A sauran wasannin kuwa, Fiji ta ba da mamaki inda ta doke Ostareliya da 22-15, lamarin da ba ta damar darewa a matsayi na biyu a rukunin C da maki shida, a bayan Wales mai maki 10. Ita kuwa Ingila da gumin goshi ne ta doke Japan da ci 34 da 12. Ita ma dai Ingila ta yi nasara karo na biyu a jere a gasar cin kofin duniya, kuma a yanzu tana da tazarar maki hudu a rukunin D a kan Samoa, abokiyar karawarta na gaba da Japan.

Gasar kasa da kasa ta guje-guje da tsalle-tsalle da ake wa lakabi da Diamond League ta kammala a Oregon na kasar Amurka, wacce ta ba 'yan wasa biyu damar kafa tarihi a fannoni daban-daban. Na farko dai ya kasance bajintar da 'yar tseren kasar Habasha ko Ethiopiya Gudaf Tsegay ta nuna na lashe tseren mita 5000 a cikin mintuna 14 cif-cif. Wannan nasarar ta bada damar juya babin tarihin da fitacciyar 'yar tseren Kenya Faith Kipyegon ta kafa a watan Yuni da ya gabata, inda ta zo na daya a cikin mintuna 14 da dakikoki biyar. Sai dai abin lura a nan shi ne, Faith Kipyegon da aka kasa dokewa a kakar wasa ta bana ba ta shiga wannan tseren ba.

Daya dan wasa da ya taka rawar gani, shi ne Armand Duplantis dan kasar Sweden wanda ya yi nasara dogara sanda wajen yin tsalle mita 6m da cm24. Wannan shi ne karo na bakwai da dan tsallen sanda mai shekaru 23 ya doke tarihin duniya tun shekarar 2020, lamarin da ke nuna karfin ikonsa a kowace rana a wannan bangare.

Deutschland Bundesliga - Bayern München v Bayer Leverkusen
Hoto: Angelika Warmuth/REUTERS

Yanzu kuma sai gasar Bundesliga inda aka gudanar da wasanni mako na hudu a karshen mako, kuma kungiyoyin biyu da suka fi fice tun da aka fara kakar wasa Bayern Munich da Bayer Leverkusen sun rabu da ci 2-2. Duk ma da cewa kowacen su na maki 10, amma 'yan wasan Xabi Alonso sune ke ci gaba da jan ragamar teburin kwallon kafa a Jamus saboda ita Leverkusen ce ta bi Yaya-babba Bayern gida kuma ta hana mata rawar gaban hantsi.

Sai dai, kungiyoyi daban-daban har guda hudu sun yi kwanton bauna da nufin neman dare samun teburi sakamakon maki tara tara da suka da shi: na farko dai akwai Leipzig da ta ci Augsburg da ci 3-0,  sai Hoffenheim da ta doke Cologne da ci 3-1, ita kuwa Stuttgart ta mamaye  Mainz da ci 3-1, yayin da Wolfsburg da ta doke Union Berlin da ci 2-1, Godiya ta tabbata da dan wasan baya na Wolsburg da ya zira kwallon yankar kauna.

Ita kuwa Borussia Dortmund, bayan canjaras biyu a jere, a wannan karon ta samu nasara a kan Freiburg da ci 4-2 , alhami a kai minti na 60 na wannan wasa ana gasa mata aya a hannu. Duk ma da cewa Yaya-karama, ba ta kama hanyar samun natsuwa ba sakamakon matsayinta na bakwai da maki takwas, amma kocinta Edin Terzic ya tabbatar da cewa kungiyar na kan kyakkyawar turba, musamman a fannin gudunmawar da 'yan wasa da ke maye gurbin.

A  sakamakon sauran wasannin kuwa, Werder Bremen ta dibi kanshinta a hannun sabon zuwa Heidenheim da ci  4-2. Sai dai Darmstadt da ta hauro babban lig din kwalon kafar Jamus ba ta samu nasararsa ba. Hasali ta tashi ci 3-3 da  Borussia Mönchengladbach. A jimlance dai, Stuttgart ta kasance kungiyar da ta fi zira yawan kwallaye a Bundesliga, inda dan wasanta  na gaba dan asalin Ghinea conakry Serhou Guirassy ke da kwallaye 8 a raga, kuma a karshen makon ne ya ci uku daga cikinsu, lamarin da ya faranta masa rai.

Fußball Europa Conference League | West Ham United - Fiorentina
Hoto: Petr David Josek/AP Photo/picture alliance

A manyan lig na kwallon kafa na nahiyar Turai kuwa, A Premier League ta Ingila,  Manchester City ta yi nasara ta biyar a wasanni biyar bayan da ta doke West-Ham da 3-1. A yanzu, Kungiyar da Pep Guardiola ke horaswa ta yi zarrar maki biyu ga kungiyoyi uku da suka hada da Tottenham da suka doke Sheffield 2-1, sai kuma Liverpool  da kuma Arsenal. Ita kuwa Brighton da ta lallasa Manchester United da ci 3-1 tana a matsayi na biyar da maki 12.

A Ligue 1 na Faransa kuwa,  Monaco ta ci gaba da zama a saman teburin duk da kunnen doki 2-2 da ta yi da Lorient. Ita kuwa Brest da ke biya mata baya da samu nasara ci 2-1 a kan Reims, yayin da Nice da ke a matsayi na uku ta shammaci Paris Saint-Germain da ci 3-2. A nata bangaren, Marseille ta zama ta hudu bayan da ta tashi 0-0 da Toulouse.

A Italiya, Inter Milan ta taka rawar gani a Derby da ta yi da AC Milan inda ta doke ta da ci 5-1 . Wannan nasara hudu a wasanni hudu, ya sa Inter Milan jagororantar teburin Serie A, kuma tana gaban Juventus da ta doke Lazio 3-1 da maki biyu. Ita kuwa Naples da ke rike da kambun zakara ta tashi 2-2 da Genoa. Neapolitans sune na biyar, maki biyar daga saman matsayi.

Athletic club de Bilbao Fußball
Hoto: Tabitha Anghel/AA/picture alliance

A Spain kuwa, Real Madrid ta samu nasara a karo na biyar a wasanni biyar da ta buga a gasar La Liga. Jagoran babban lig Spain na gaban FC Barcelona da maki biyu (duk da ya doke Betis da ta yi da 5-0). Ita kuwa  Athletic Bilbao da ta samu nasara ci 3-0 a gaban Cádiz na a matsayi na uku. A nata bangare, Valencia ta doke Atletico Madrid da ci 3-0, lamarin da ya jefa ta a matsayi na biyar da maki tara.

Sai dai duk wannan sabata juyata da ake yi a manyan lig na kasashen Turai, ma'abota kwallon kafa na Jamhuriyar Nijar ba sa shaidarwa sakamakon katse kafofin yada labarai na Faransa da ke haska wadannan gasanni. Sai dai baya baya ga haddasa damuwa da wannan mataki ke yi a tsakanin matasa da ke daukar kwallon kasashen Turai a matsayin nishadi, amma ya sa masu sha'awar kwallon yin buris da kungiyoyin kwallon kafar Faransa sakamakon takun sakar diflomasiyya da ke tsakanin hukumomin mulkkin sojin Nijar da tsofuwar uwargijiyarsu Faransa.

Kungiyar Huracanes FC ta Equatorial Guinea ta kasance ta karshe da ta cancanci shigar gasar cin kofin zakarun matan Afirka sakamakon yin wajen road da TP Mazembe ta Kwango. Wannan ne ya ba wa Hukumar kwallon kafar nahiyar Afirka CAF damar sanin sunayen kungiyoyi takwas da za a fafata da su a Côte d' Ivoire  daga ranar 5 zuwa 19 ga watan Nuwamba, a gasar Champions lig ta mata da ke zama na uku. Hasali ma dai, AS FAR ta Maroko mai rike da kofin gasar, da Mamelodi Sundowns na Afirka ta Kudu na daga cikin wadanda suka cancanci shigara gasar ta mata, inda kungiyoyi biyar za su halartar a karon farko ciki har da Athlético d'Abidjan.

Ita AS FAR  da Mamelodi Sundowns na fatan lashe wannan kofi a karo na biyu a jere, lamarin da zai ba su damar lashe dala Amirka 400,00. Ita dai CAF tana son amfani da gasar zakarun mata wajen bunkasar kwallon kafa na mata a nahiyar Afirka.