1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniJamus

Labarin wasanni 25.9.23

Suleiman Babayo AH
September 25, 2023

A wasannin Bundesliga Bayern Munich ta yi wa Bochum cin kacar tsohon keke rakacau, 7 da nema a wasan na karshen mako yayin da a . A wassanin lig na La Liga na Spain, Girano ta doke Mallorca 5 da 3,

https://p.dw.com/p/4Wm8c
Hoto: Thilo Schmuelgen/REUTERS

 

Kungiyar kwallon kafa ta Ajax da ke kasar Netherlands ta sallami daraktan kungiyar Sven Mislintat, sakamakon rudanin da aka smau a filin wasa a wannan Lahadi da ta gabata, lokacin da Fayenoord take jefa kwallaye uku a ragar Ajax, abin da ya janyo magoya bayan kungiyar suka tayar da hatsaniya lamarin da ya tilasta 'yan sanda amfani da hayaki mai saka hawaye. A wassanin lig na La Liga na Spain, Girano ta doke Mallorca 5 da 3, Barcelona ta doke Celta 3 da 2, sannan Real Sociedad ta doke Getafe 4 da 3, kana Atletiko Madrid ta samu galaba kan Real Madrid 3 da 1, yayin da Osasuna ta Sevilla suka tashi cancaras. A wasannin lig na Premier da ake karawa a Ingila, Manchester United ta bi Burnley har gida ta doke ta 1 mai ban haushi, haka Everton ta bi Brentford ta doke ta 3 da 1, sannan Aston Villa ta yi irin wannan sa'ar wajen bin Chelsea har gida ta doke ta 1 da nema, sai dai kungiyar Sheffield United ta yi irin wannan babbar sa'a wajen bin Newcastle gida ta yi mata raga-raga 8 da nema.

Bundesliga Bayer Munich ta yi Bochum rabani dfa yaro

Fußball Bundesliga | VfL Bochum - FC Bayern München
Hoto: Neundorf/Kirchner-Media/IMAGO

A wasan lig na Jamus na Bundesliga, Augsburg ta doke Mainz 2 da 1, Leipzig ta bi Moechengladbad gida ta lallasa ta 1 da nema, haka ita ma Hoffenheim ta bi Union Berlin gida ta doke ta 2 da nema. Sannan Dortmund ta samu galaba kan Wolfsburg da ci 1 mai ban hasuhi, yayin da Werder Bremen ta doke FC Kolon 2 da 1, ita kuwa Leverkusen ta yi lagalaga da Heidernheim 4 da 1, ana bangaren Frankfurt ta tashi babu ci da kungiyar Freiburg. Kana kungiyar Bayern Munich ta yi wa Bochum cin kacar tsohon keke rakacau, 7 da nema a wasan na karshen mako.

Wasannin zari rugha na duniya a Faransa Wales ta doke Ostiriliya

Kenya Cup Rugby
Hoto: IMAGO/Kevin Manning

A wasan cin kofin duniya na zari ruga da ke wakana a kasra Faransa, Wales ta samu gabala kan Ostiriliya 40 da kuma 6, haka ita Ireland ta doke Afirka ta Kudu 13 da 8. Yanzu haka a rukunin farko mai masaukin baki Faransa ke jagoranci da maki 13 yayin da Italiya ke mara mata baya da maki 10 sai New Zealand mai maki 5, sannan kasashen Uruguay da Namibiya ba su da maki ko daya. Kana a rukuni na biyu Ireland ke jagoranci da maki 14, sannan Afirka ta Kudu a matsayi na biyu da maki 10 sai Scotland a matsayi na uku da maki 5, yayin da kasashen Tonga da Romaniya ba su da maki ko daya. A rukuni na uku na wasan na Zari-ruga na duniya , Wales ke jagoranci da maki 14, sai Fiji na a  maki 6 da Asutarliya ita ma maki 6 sannan Georgia da Portugal ko wace maki 2. A rukuni na hudu Ingila ke kan gaba da maki 14, sannan Samoa da maki biyar haka ita ma Japan tana da maki 5 sai Ajentina mai maki 4 a karshe kuma akwai Chile wace ba ta da maki ko daya. An fara gasar wasanni na yara kasa da shekaru 15 a birnin Asaba Jihar Delta a Najeriya. Yaran dai da ke shiga gasar, tuni su ka hallara a filin wasa na Stephen Keshi da ke jahar ta Delta,da nufin wakiltar jahohin su a gasar. Gasar dai ta National Youth Games na da nufin gudana ne duk shekara,da kuma ke da nufin ganowa tare da ba da kwarin gwiwa ga ma su kwazo, da ka iya cin nasarori a gasar wasanni ta gida da ma kasashen Duniya.