1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moroko za ta dauki nauyin wasan Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar SB/MA
October 2, 2023

Kungiyyoyin Darmstadt da Heidenheim sun yi rawar gani a karshen mako, yyin da FC Kolon ta gaza katabus a gida a hannun Stuttugart.

https://p.dw.com/p/4X3G5
Jamus I Darmstadt da Werder Bremen
Wasan Darmstadt da Werder BremenHoto: Thomas Voelker/IMAGO

Fitaccen dan damben Kamaru haifaffen Faransa Cédric Doumbé ya sake kafa tarihi, inda a fafatawar da suka yi da Jordan Zebo a karshen mako ya kammala wasan tare da samun nasara a turmin farko cikin dakika tara. Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan nasarar da yayi, mai shekaru 31 a duniya Doumbé ya bayyana kansa a matsayin kwararre a wannan fage na dambe ajin masu nauyi.

Kungiyar kwallon Golf ta kasashen Turai ta yi nasarar sake lashe gasar cin kofin Ryder, godiya ga fitaccen dan wasan nan dan kasar Ingila Tommy Fleetwood. Fleetwood ya tabbatar da ganin kambun kwallon Golf na duniya ya sake dawowa Turai. Wannan dai ya sanya Turai ta haura tarihin da ta kafa na nasara a wasanni 30 da ta fafata a gida, kana ramuwar gayya ga cin kacar da Amurkawan suka yi musu a shekara ta 2021 da ci 19 da daya.

Dan gudun fanfalake na kasar Chaina Xie Zhenye ya lashe kambun tseren mita 100 na maza, a gasar wasannin nahiyar Asiya da ke gudana a Chaina. Xie dai ya kammala tseren ne a kasa da dakika 10, yayin da Puripol Boonson dan kasar Thailand ya kammala nasa tseren a matsayin na biyu cikin dakika 10 kana Muhd Azeem Fahmi na Malasiya ya zo na uku a fafatawar da suka yi a filin wasan guje-guje da tsalle-tsalle na birnin Hangzhou da ke Chaina.

Jamus | Heidenheim da Werder Bremen
Wasan Heidenheim da Werder BremenHoto: Tom Weller/dpa/picture alliance

A gasar Bundesliga ta Jamus kuwa, a karshen mako kungiyoyin kwallon kafa na Heidenheim da Darmstadt ne suka kafa tarihi, inda suka hauro daga rukuni na biyu kuma suka bai wa tsofaffin hannu mamaki a fafatawarsu. A wasannin mako na shida na kakar Bundesliga ta bana, Dortmund ta bi Hoffenheim har gida tare da lallasata da ci uku wa daya, kana Heidenheim ta karbi bakuncin Union Berlin ta caskara ta da ci daya mai ban haushi yayin da aka tashi wasa tsakanin RB Leipzig da Bayern Munich canjaras biyu da biyu.

Leverkussen ta bi Mainz har gida ta kuma lallasa ta da ci uku da nema kana Frankfurt ta sha kashi a gidan Wolfsburg da ci biyu da nema. Ita ma Bochum ta yi abin fadi a gida ta hanyar karbar kwallaye uku a raga daga Borrussia Mönchengladbach yayin da ta samu damar zura kwallo daya tilo a ragar bakin nata. Ita kuwa FC Kolon abin kunya take kara yi, domin kuwa ta sha kashi a gida da ci biyu da nema a hannun Stuttgart. Freiburg ta karbi bakuncin Ausburg ta kuma lallasata da ci biyu da nema, yayin da wasan da ya fi bayar da mmaki shi ne yadda Darmstadt ta huce haushinta a kan Werder Bremen da ta kai ziyara da ci hudu da biyu. A yanzu haka dai Bayern Munich ta sauko zuwa matsayi na uku ta teburin kakar ta bana, yayin da Leverkussen ke a matsayi na daya kana Stuttgart na a matsayi na uku.

 Manchester United ba ta ji da dadi ba, domin kuwa Crystal Palace ta bi ta har gida ta kuma lallasa ta da ci daya mai ban haushi
Wasan Manchester United da Crystal PalaceHoto: Dave Thompson/AP Photo/picture alliance

A gasar Premier League ta Ingila kuwa, Manchester City ta sha mamaki a karshen mako, bayan da ta ziyarci gidan kungiyar Wolverhampton ta kuma sha kashi da ci biyu da daya. Ita kuwa Tottenham ta karbi bakuncin Liverpool ta kuma caskara ta da ci biyu da daya kana Arsenal ta bi Bournemouth har gida ta kuma yi mata dukan kawo wuka da ci hudu da nema. Manchester United ba ta ji da dadi ba, domin kuwa Crystal Palace ta bi ta har gida ta kuma lallasa ta da ci daya mai ban haushi. A yanzu haka dai Manchester City ke saman teburin na Premier ta Ingila yayin da Tottenham ke biye mat a matsyi na biyu kana Arsenal ke a matsayi na uku.

Maroko ta samu nasarar karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON a shekara ta 2025, yayin da kasashen Kenya da Tanzaniya da kuma Yuganda za su karbi bakuncin gasar a shekara ta 2027.