1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekarar 2020 ta kasance mai hadari ga 'yan jarida

December 30, 2020

Kungiyar Reporters Without Borders ta ce sama da 'yan jarida 50 ne suka hallaka a 2020 mai karewa, inda aka yi wa wasu kisan gilla bisa sun gudanar da bincike a cikin aikinsu na jarida.

https://p.dw.com/p/3nNfg
Symbolbild Pressefreiheit
Hoton gangamin yaki da cin zarafin 'yan jarida a FaransaHoto: picture-alliance/dpa

Shekarun uku a jere ana fuskantar yawaitar yi wa 'yan jarida kisan gilla, domin ko a shekarar 2019 da ta gabata manema labaran 53 ne aka hallaka. Wani abin da ya banbanta a wannan shekarar da sauran shekarun baya, shi ne kisan wulakancin da aka yi wa 'yan jarida kuma abin mamaki, a kasashen da babu alamun yaki. Duk da cewa duniya ta fuskanci annobar Coronavirus inda 'yan jaridun suka bayar da gudunmuwarsu wajen yaki da ita gami da kasashen da ake fama da tashe-tashen hankulla, amma wadannan bala'oi basu yi ajalin 'yan jarida ba kamar yadda kokarin bankado gaskiya ya hallakasu.

Kisan 'yan jarida ya ta'azzara a cewar RSF

Reporter ohne Grenzen Logo
Hoton kungiyar 'yan jarida ta RSFHoto: Getty Images/AFP/B. Guay

Mai magana da yawun kungiyar Reportuers Sans FrontiersRSF Pauline Ades-Mevel ita ce ta bayar da bayanan da rahotan ya kunsa, ta ce ''Rahoton kungiyar ya nuna cewa yawan 'yan jaridadar da aka kashe a fadin duniya a wannan shekarar ta 2020 ya haura 50 wanda hakan abin damuwa ne duk kuwa da cewa bara 53 suka hallaka.''   

Karin Bayani: Garkame 'yan jarida a kurkuku saboda binciken corona

Kisan 'yan jarida ya fi ta'azzara ne a kasashen da babu yaki da kaso 68%, hakan ya nuna cewa dunbin manema labarai da ke fagen daga sun fi samun cikakkiyar kariya fiye da wadanda ke tsage gaskiya komin dacinta, kowa na tuna irin yadda aka rataye wani dan jarida a Tehran mai suna Ruhollah Zam bisa tuhumarsa da aikata laifi.

Kasar Mexico ta fi zama bala'i ga 'yan jarida

Pakistan - Zeitung
Hoton jaridar DAWN a PakistanHoto: Getty Images/AFP/R. Tabassum

Rahoton ya zargi gwamnatocin da suka daurewa cin hanci da rashawa gindi, da kuma daidaikun al'umma masu aikata miyagun laifuffuka da yin kisan. Kasar Mexico ne aka fi samun koma baya a fannin 'yancin aikin jarida, kuma kasar ta kasance makabartar 'yan jarida da aka yi wa kisan wulakanci a wannan shekara, inda ake samun gawarwakin 'yan jaridar da aka cirewa kai ko a yi masu gunduwa-gunduwa, lamarin da nuna cewa ita ce kasa ma fi muni a duniya, domin 'yan jarida 8 ne suka rasa rayukansu, a shekarun 2018 da 2019 an samu mutuwar wasu kimanin 10, hakan kuma kisan na bana na zama wani muhimmin sako ga 'yan jarida masu binciken kwakwaf da su shiga taitayinsu.

Karin Bayani: DW ta karrama masu ba da labarai kan Corona

A fayyace 'yan jarida 10 ne aka kashe sakamakon rahoton da suka bayar na cin hanci da yin ruf da ciki da dukiyoyin al'umma, yayin da aka hallaka wasu uku saboda sun bayarda rahotannin yin ba daidai ba a bangaren muhalli da hakar ma'adanai.