1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Mexiko an fi kashe 'yan jarida

Abdourahamane Hassane
December 29, 2020

A rahoton ta na shekara da ta bayyana kungiyar 'yan jaridu na kasa da kasa Reporters without Borders ta ce a wannan shekara ta 2020 da ke shirin karewa 'yan jaridu guda 50 aka kashe a duniya.

https://p.dw.com/p/3nJ2p
Deutschland Berlin Reporer ohne Grenzen protestieren
Hoto: picture-alliance/ZUMA Press/J. Scheunert

Kasashen Siriya da Yemen da Irak da Afghanistan na daga cikin kasashen da 'yan jaridar suka taras da ajalin su a lokacin da suke gudanar da aiki. Kungiyar ta RSF ta ce Mexiko ita ce ta fi kashe 'yan jaridar har guda takwas a wannan shekara, sai Indiya  da Pakistan dada Honduras.