1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya

Zainab Mohammed Abubakar
May 3, 2020

A yayin da ake bukin ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya, aikin jarida a Masar ya kasance tamkar aikata mugun laifi ne, inda hukumomi ke yiwa kafofin yada labaru bita-da-kulli da capke 'yan jarida

https://p.dw.com/p/3bhoY
Deutschland Symbolbild Pressefreiheit
Hoto: Imago Images/S. Boness

Rahoton kungiyar kare hakkin jama'a ta kasa da kasa ta Amnesty International data wallafa a wannan Lahadi ya nunar da haka.

A dai dai lokacin da yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus ke karuwa, gwamnatin masar na kara tsananta ikonta kan toshe hanyoyin samun bayani, maimakon barin duniya ta san gaskiyar halin da ake ciki game da lafiyar al'umma, a cewar kungiyar Amnesty mai matsugguni a birnin London.

Tuni dai hukumomin kasar suka yi gargadin cewar, duk dan jaridan da ya kalubalanci bayanan gwamnati, zai fuskanci hukunci mai tsanani, a cewar Philip Luther, darektan kungiyar na yankin Gabas ta Tsakiya da yankin Arewacin Afirka.

Amnesty ta bada misallin 'yan jarida 37 da a yanzu haka ke tsare, a kan zargin abun da gwamnatin Masar din ta kira " Yayata bayanan karya ko kuma  saba ka'idojin amfani da shafukan sada zumunta na zamani".