1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Me nene asalin tushen Coronavirus?

April 21, 2020

Masu nazarin bincike da 'yan jarida sun shafe  watanni suna hasashe game da tushen kwayar cutar Coronavirus, kan cewa ko ta samo asali ne daga birnin Wuhan na kasar Chaina.

https://p.dw.com/p/3bE0c
China Wuhan Rückkehr zur Normalität
Masana a Chaina na kokarin samo maganin cutar CoronavirusHoto: AFP

Ko da yake har yanzu ba a tantance asalin inda cutar ta faro ba, amma binciken wasu masana kimiyya a Chaina na kokarin samar da allurar magance cutar. Sai dai kuma kafofin yada labarai na yammacin Turai suna bayar da labarin cewa mai yiwuwa tushen kwayar cutar ta samo asali ne daga wata cibiyar binciken kwayoyin cutattuka a Wuhan. Irin wadannan hasashe sun yi ta yawo a kafofin sada zumunta na zamani tun a watan Janairu, inda aka rika danganta bayanan samuwar cutar da dakin binciken kimiyya na sojojin Chaina wajen kirkirar kwayoyin halitta masu hadari domin makami mai guba.

Jemage ya yada COVID-19 ga mutane

Riesenfledermaus beim Winterschlaf in Polen
Jemagu ne suka yada Coronavirus Hoto: Imago Images/blickwinkel/AGAMI/T. Doumax

Fabian Schmidt na sashen kimiyya na nan DW ya ce ko kadan babu gaskiya a cikin irin wannan tunani, tabbataccen batu shi ne cutar ta samo asali ne daga jikin jemage kuma ta yadu zuwa jikin dan Adam, yana mai cewa: "Sam kwayar cutar ba kirkirar ta aka yi a dakin binciken kimiyya ba, mai yiwuwa an shigar da kwayar cutar ne sakamakon ayyukan bincike akanta, kuma a haka wani ya kamu da ita sannan ta yadu. Abin da yake a fayyace shi ne cutar ta samo asali ne daga jemage. Suna daukar kwayar cutar saboda garkuwar jikinsu na da karfi kuma kwayar cutar na iya habaka a jikinsu, saboda halittarsu suna iya jurewa su rayu ba tare da ta yi musu wani lahani ba, shi yasa suke iya daukar cututtuka da dama kamar yadda masana kimiyya suka tabbatar.

Binciken wata tawagar masana kimiyya karkashin jagorancin Farfesa Kristian G Anderson ya tabbatar da wannan, cikin mukalar da ya wallafa a watan Maris a mujallar kimiyyar yanayi da magunguna. Hasali ma ayyukan cibiyar binciken ta Wuhan ba abu ne boyayye ba, domin ta sha wallafa bincikenta kan kwayoyin cututtuka masu nasaba da jemagu a sahihan mujallu na duniya, tare da wasu cibiyoyin bincike na yammacin Turai.

Pakistan Karachi Haustiere von Lockdown bedroht
Dabbobin gida ba sa yada CoronavirusHoto: AFP/A. Hassan

Ko dabbobi kamar na gida ka iya yada cutar Coronavirus? Fabian Schmidt ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike, amma abin da aka sani shi ne wasu dabbobin kamar kare ko alade ba sa yada cutar Coronavirus, kamar Binciken masana kimiyya na kasar Chaina ya nunar, haka ma kaji ko agwagi. Binciken da aka gudanar a Jamus ma a kan mutanen da suka kamu da cutar kuma suke da mage a gida, ba a samu wata hujja da ta nuna mage na iya yada cutar ba, saboda haka babu wata fargaba akan wadannan dabbobi a wannan lokaci.

Kyakkyawan fata ga Afirka

To ko wace fargaba ce ake da ita game da cutar a nahiyar Afirka? Fabian Schmidt ya ce: "Ina tsammanin babban hadarin da ake da shi a Afirka shi ne mutane da ke zaune cunkushe a wuri guda da mutane da dama da ke amfani da motocin haya, to amma ya kamata mu gane wannan cutar ba kamar Ebola ba ce wadda ke iya halaka mutane nan da nan, wannan cutar ta fi kama mutanen da ke da yawan shekaru da kuma ke da tarihin wata cuta a baya. Irin wadannan mutane ya kamata su yi kokari su zauna a gida, matasa kuma su ci gaba da daukar matakan tazara a tsakanin juna da yawan wanke hannu, amma ina da kyakkyawan fata ga Afirka cewa cutar ba za ta yi wani mummunan lahani ba."