1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Makomar Turai da Afirka

Suleiman Babayo
January 19, 2024

Matasan 'yan jarida daga kasashe 15 na nahiyar Afirka da suka hada da Najeriya da Kenya sun hallara a Jamus domin gasar rubutu kan makomar Afirka

https://p.dw.com/p/4bU3V
Wasu daga cikin Jaridun Jamus
Wasu daga cikin Jaridun JamusHoto: Hartmut Schmidt/imageBROKER/picture alliance

Za mu fara da jaridar die Tageszeitung wadda ta yi sharhi mai taken makomar Turai da Afirka, game da taro cikin wannan wata na Janairu a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, da aka gayyaci matasan 'yan jarida 15 daga kasashen nahiyar Afirka da suka hada da Najeriya, da Kenya, gami da Afirka ta Kudu karkashin wata gidauniya kan gasar rubutu bisa makomar nahiyar Afirka. A gaba daya za a duba irin tasirin nahiyar Afirka, da suka hada da yaki da sauyin yanayi da yaki da 'yan Jihadi gami da kawar da talauci da rikice-rikice, tare da samar da manufofin ci gaba da bunkasa tsarin dimukaradiyya a nahiyar.

A daya bangaren jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta duba yadda kwararar bakin haure da masassarar tattalin arziki suke kara karfafa masu matsananci ra'ayi na jam'iyyar AfD ta Jamus. Galiban baki na shiga daga kasashe masu tasowa na Afirka wadanda suke daukar kasadar shiga kasashen Turai, abin da ke kara matsin lamba ga gwamnatocin Turai kamar Jamus karkashin shugaban gwamnati Olaf Scholz.

Karin Bayani: Jamus: Bukatar garambawul kan dokar bakin haure

Ita kuwa Der Spiegel ta ce Tekun Bahar Rum na zama daya daga cikin wurare masu hadari na duniya, a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya. A cewar hukumar kimanin bakin haure 710 suka halaka a cikin tekun a kokarinsu na zuwa Turai, a shekarar da ta gabata, lamarin da ya nuna ninki idan aka kwatantan da shekarar da ta gabace ta. Wannan alkaluman wani bangare ne na abin da yake faruwa cikin tekun. Kasashen musamman Cyprus da Girka ke zama matakin farko da bakin haure ke neman kai wa domin tserewa daga rikice-rikice da tashe-tashen hankula gami da talauci a kasashen Gabas ta Tsakiya da nahiyar Asiya gami da nahiyar Afirka, a kokarin samun rayuwa mai inganci a kasashen Turai. Haka bakin hauren na neman shiga ta wasu bagarorin na Girka da Italiya.

Karin Bayani:Taron tattalin arziki tsakanin Turai da Afirka

Haka wasu hanyoyin daga bangaren arewacin Afirka na cikin inda bakin haure ke bi domin shiga kasashen Turai ta tekun Bahar Rum ta kasar Spain. Wata ta bayyana cewa kimanin bakin haure 6,618 suka halaka a kokarin shiga Spain a shekara ta 2023, kana wasu 2,390 suka halaka a shekara ta 2022 a cewa kungiyar mai zaman kanta.

Sai jaridar Neue Zürcher Zeitung ta duba yadda aka samu mahalarta da dama daga kasashen Afirka da wasu sassa a taron kasuwanci na duniya da ke gudana na shekara-shekara a Davos da ke kasar Switzerland. Jaridar ta bayyana irin tasirin da taron yake da shi inda ake samun shugabannin manyan kamfanoni na duniya da ke halarta gami da shugabanni na siyasa da masu tafiyar da harkokin tattalin arziki na duniya.