1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Bukatar garambawul kan dokar bakin haure

December 26, 2023

Tsohon mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel, ya soki matakan da hukumomin Jamus ke bi wajen tunkarar matsalolin bakin haure, inda ya ce Jamus ta gaza wajen killace bakin haure.

https://p.dw.com/p/4aaVh
Hoto: Lisi Niesner/REUTERS

Tsohon jagoran jam'iyyar SPD kuma tsohon mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel, ya soki matakan da hukumomin Jamus ke bi wajen tunkarar matsalolin bakin haure, inda ya ce Jamus ta gaza wajen killace bakin haure.

Gabriel ya ce al'ummar Jamus na bi sau da kafa kan abubuwan  da ke faruwa wajen kwararar bakin haure da masu neman mafaka a kasar, da hakan ke za me mata barazana ta fuskar tsaro, kamar yadda ya shaidawa jaridar Neue Osnabrücker Zeitung, a wayewar garin yau.

Ya kuma bukaci hukumomin Jamus da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun bujiro da tsare-tsaren shige da ficen bakin haure da 'yan gudun hijra harma da masu neman mafaka gabanin zaben kungiyar kasashen tarayyar Turai a shekara mai kamawa.

Daga watan Janairu zuwa Nuwambar 2023, akalla mutum dubu 305 ne suka mika takardar bukatar neman mafaka a Jamus, a karon farko da hakan ya kai ga karin kaso 60% na masu neman mafakar idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.