1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Scholz: Gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da ayyukanta

Zainab Mohammed Abubakar
November 28, 2023

Shugaban gwamnatin Jamus ya yi alkawarin ceto kasar daga rikicin kasafin kudin da ya dabaibaye gwamnatinsa, yayin da ya gaza gabatar da gamsassun bayanai kan yadda za a toshe gibin kasafin biliyoyin Euro.

https://p.dw.com/p/4ZYCh
Olaf ScholzHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Wannan matsala dai ba za ta shafi kudaden da ake kashewa a yanzu ba, inda Olaf Scholz ya tabbatar wa 'yan majalisar dokoki ta Bundestag a wannan Talatar (28.11.23) cewa,  gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da ayyukanta.

Sai dai jawabin shugaban gwamnatin na Jamus, ya gaza fayyace yadda za a shawo kan matsalar wagegen gibin, bisa ga hukuncin da wata babbar kotun kasar ta yanke a farkon wannan watan ba, wanda ya janyo suka daga jam'iyyun adawa.

Ya tabbatarwa da Jamusawa cewar, ko kadan hukuncin kotun tsarin mulkin, ba zai canza komai ba a rayuwarsu ta yau da kullum, a yanzu da ma nan gaba, a bangaren tallafin yara ko tallafin karatu da fensho ko tallafin biyan haya.