1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamhuriyar Benin ta sake bude kofofinta ga 'yan Nijar

Gazali Abdou Tasawa M. Ahiwa
December 28, 2023

'Yan kasuwa da ma wasu sauran 'yan kasa a Jamhuriyar Nijar, na martani kan matakin kasar Benin na dage haramcin sauke hajojin 'yan kasuwan Nijar a tashar ruwan Cotonou.

https://p.dw.com/p/4afCk
Tashar ruwa a birnin Cotonou
Tashar ruwa a birnin CotonouHoto: Getty Images/P. Dagnitche

A watan Oktoban da ya gabata ne hukumar tashar ruwan Cotonou ta dauki matakin haramta sauke hajojin 'yan kasuwan Nijar a tashar, lamarin da ya tilasta masu kewayawa ta kasashen Togo da Burkina Faso domin shigo da hajojin nasu a cikin gida.

A wata takarda ce da babban daraktar tashar ruwan Cotonou ya sanya wa hannu a ranar 27 ga wannan wata na Disamban 2023, kasar ta Benin ta sanar da dage haramcin sauke kayan da 'yan kasuwar Nijar suke sayowa daga ketare suna shigo da su gida ta tashar ruwan ta Cotonou mai nisan kilomita dubu da kuma amma ke zama mafi kusa ga kasar ta Nijar.

Hukumar tashar ruwan Cotonoun ta ce da ma a baya ta dauki matakin haramta sauke hajojin Nijar din ne sakamakon yadda takunkumin tattalin arzikin da kungiyar ECOWAS ta saka wa Nijar din bayan juyin mulki da matakin rufe iyakoki ya sanya 'yan Nijar suka kasa kwashe hajojin nasu wadanda suka makare tashar ruwan har babu wani wuri iya ajiye su.

Hada-dahar kasuwa a birnin Niamey na Nijar
Hada-dahar kasuwa a birnin Niamey na NijarHoto: B.Hama/AFP/GettyImages

Amma bayan da 'yan kasuwan Nijar suka fice da wasu daga cikin kayan nasu ta hanyar Lome, a yanzu an samu sarari a tashar wanda zai iya bai wa 'yan Nijar din damar ci gaba da shigo da hajojin nasu ta tashar ruwan Cotonou.

To sai dai Alhaji Yacouba dan Maradi shugaban kungiyar manyan 'yan kasuwa ta SIEN ya ce da ma sun san a rina amma babu tabbas su ci gaba da aiki da Cotonou.

Shi kuwa Alhaji Salissou Amadou, dan kasuwa kuma dan fafutika a Nijar na ganin kasar Benin ta bude tashar ruwan ce domin cin moriyar man fetir da Nijar za ta fara fitarwa a sabuwar shekara ta hanyar ruwan Cotonoun zuwa kasuwannin duniya.

Sai dai wasu 'yan Nijar din na ganin matakin bude tashar ruwan Cotonoun ga ‘yan kasar abun a yaba ne kuma wata alama ce ta kusan shawo kan matsalar Nijar da ECOWAS. Onorabul Ousmane Abdourahmane wani dan siyasa na daga cikin masu irin wannan tunani. 

Yanzu dai 'yan Nijar sun kasa kunne su ga amsar da hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar za su bai wa kasar ta Benin a game da wannan tayi da suka yi wa Nijar din an sake komawa aiki da tashar ruwan Cotonoun.