1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Martani kan bude iyakar Benin

Gazali Abdou Tasawa LMJ
December 21, 2023

Sa'o'i kalilan bayan da shugaban kasar Jamhuriyar Benin ya bayyana aniyarsa ta bude iyakar kasarsa da Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka, kungiyoyin manyan 'yan kasuwar Nijar din sun fara bayyana ra'ayoyinsu kan batun.

https://p.dw.com/p/4aSK7
Nijar | Juyin Mulki | Sojoji | Kan Iyaka | Najeriya | Benin | 'Yan Kasuwa
Ba dai kan iyakar Najeriya da Benin ne kadai aka rufe ba, har ma da iyakarta da NajeriyaHoto: Mohammed Babangida/AP/dpa/picture alliance

A yayin da wasu 'yan kasuwar na Jamhuriyar Nijar ke maraba da matakin bude kan iyakar da Shugaba Patrice Talon na makwabciyarsu Jamhuriyar Benin ya ce zai yi da kuma bayyana fatan tabbatuwarsa ba da jimawa ba, wasu kuwa sharadi suka fara dora wa hukumomin kasar Benin din kan ka'idojin kwashe hajojinsu da ke jibge a babbar tashar ruwan Cotonou. A wani jawabi da Shugaba Talon ya yi a majalisar dokokin kasarsa ne ya bayyana aniyar tasa ta gaggauta mayar da hulda da kasashe makwabtanta wadanda aka yi juyin mulki musamman Nijar, wacce kungiyar ECEOWAS ko CEDEAO ta kargama wa takunkumin tattalin arziki mafi tsanani da ya shake kasar sama da watanni hudu ke nan.

Burkina Faso: Abinci zuwa Nijar

Da yake tsokaci kan wannan albishir na shugaban kasar ta Benin, Alhaji Illa Hatumi Mai Aya shugaban kungiyar 'yan kasuwar Nijar, bayyana gamsuwarsa ya yi da matakin da ya ce zai taimaka a samu sa'ida a kasar. To sai dai a nata bangare babbar kungiyar Manyan 'Yan Kasuwan Nijar ma su Shigo da Kaya daga Ketare ko Fitar da su, ta bakin shugabanta Alhaji Sani Shekaraou ta ce akwai bukatar ba tare da wani sharadi ba mahukuntan na Benin su fara cire kudin ajiyar dubban motocin dakon hajojin 'yan kasuwar Nijar din da suka makale a tashar ruwan Cotonou, ko da za su bude iyakar tasu.

Yadda katse lantarkin Najeriya ya shafi Nijar

Rufe iyakar Benin da Nijar na zaman guda cikin dalilin karuwar farashin kaya da ma karancinsu, a kasuwannin Nijar din. A kan haka ne kungiyar ADDC Wadata mai yaki da tsadar rayuwa ta bakin shugabanta Malam Maman Nouri ta bayyana fatan ganin tabbatar wannan mataki cikin gaggawa, domin kawo karshen wannan matsala. Yanzu dai al'umma sun zura idanu su ga ko mahukuntan Nijar din za su amince da matakin Benin na bude iyakar tata, musamman ta la'akari da sharadin shugaban kasar Benin din na ganin sojojin da asuka yi juyin mulki sun cika ka'idojin da kungiyar ECOWAS da sauran kasashen duniya suka gindaya musu kafin mayar  da hulda a tsakanin kasashen biyu.