1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNijar

Tashar ruwa ta Cotonou ta daina karbar hajojin Nijar

Gazali Abdou Tasawa MAB
October 27, 2023

Manyan 'yan kasuwa na Nijar da ke shigo da hajoji daga ketare sun yi martani kan umurnin da Jamhuriyar Benin ta bayar na kwashe hajojinsu da ke jibge a tashar ruwan Cotonou tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki.

https://p.dw.com/p/4Y6wf
NIjar ta dogara kan tashar ruwan Cotonou wajen shigo da hajojinta
NIjar ta dogara kan tashar ruwan Cotonou wajen shigo da hajojintaHoto: Getty Images/P. Dagnitche

Babban daraktan tashar ruwan Cotonou na Jamhuriyar Benin ya ce kasarsa ba za ta ci gaba da karbar hajojin Nijar ba, duk da cewa ita ce mafi kusa da birnin Yamai. Wannan tashar ruwan da ke a nisan kilomita sama 1000 dubu da babban birnin Nijar , amma 'yan kasuwa sun fi amfani da ita wajen shigo da hajoji daga ketare. Tun bayan da sojoji suka kifar da zababbiyar gwamnatin Mohamed Bazoum ne kasar ta Benin a bisa umurnin kungiyar ECOWAS ta dauki matakin rufe iyakarta da Nijar, lamarin da ya ritsa da tarin hajojin 'yan kasuwan Nijar.

Karin bayanNijar da Benin za su hada karfi a kan makamashii: 

Manyan motoci da ke dauke da hajoji ba sa samu sukunin ketare iyakoki zuwa Nijar
Manyan motoci da ke dauke da hajoji ba sa samu sukunin ketare iyakoki zuwa NijarHoto: Mohammed Babangida/AP/dpa/picture alliance

A lokacin da yake tsokaci kan wannan mataki, Alhaji Sani chekaraou da ke zama shugaban kungiyar 'yan kasuwar Nijar masu shigo da kaya daga ketare cewa ya yi za su dauki matakan ficewa da hajojinsu daga Jamhuriyar Benin ba tare da ba ta lokaci ba. Shi kwa Alhaji Yacouba Dan Maradi da ke shugabantar kungiyar 'yan kasuwan Nijar ta SEIN cewa lokaci ne ya yi na 'yan kasuwar Nijar su fara tunanin karkatar da akalarsu zuwa wasu tashoshin ruwa. Ita kuwa kungiyar ADDC-wadata mai yaki da tsadar rayuwa a Nijar ta bakin shugabanta Mamane Nouri cewa ta yi akwai bukatar tattaunawa domin bai wa 'yan kasuwa damar karshe ta kwashe kayansu da ke jibge a tashar ruwan Cotonoun zuwa gida.

Karin bayani: Nijar: Shirin yanke huldar tsaro da Benin

Tashar ruwan Lome da ke Togo ce za ta fara karbar kayayykin Nijar
Tashar ruwan Lome da ke Togo ce za ta fara karbar kayayykin NijarHoto: Imago/photothek

Wani rahoton Bankin Duniya ya nunar da cewa tuni tashar ruwa Lome na kasar Togo ta fara cin gajiyar hajojin Nijar da suka fara kaurace wa tashar ruwan Cotonou ta Benin a sakamakon rufe iyakar da ta hada kasashen biyu tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata a kasar Nijar.