1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar na takaddama da ECOWAS da Najeriya

Salissou Boukari LMJ
December 14, 2023

Hukumar mulkin soja ta Nijar ta fitar da sanarwa da ke kalubalantar matakin ECOWAS na bai wa tsofaffin ministocin hambararriyar gwamnati damar halartar taronta na karshe, duk da dakatar da Nijar daga cikinta.

https://p.dw.com/p/4a9Li
Nijar | Yamai | Sojoji | Abdourahamane Tiani
Shugaban gwamnatin juyin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar Abdourahamane TianiHoto: Télé Sahel/AFP

Hukumar mulkin sojan ta Jamhuriyar Nijar ta yi suka kai tsaye cikin sanarwar tata ga shugaban Najeriya wanda shi ne shugaban kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEA, sakamakon zargin da take wa Abujar da bai wa manyan jami'an hambararriyar gwamnatin Nijar din mafaka da zimmar tarwatsa Nijar duk kuwa da cewa ana neman su a kasarsu ruwa a jallo.

Karin Bayani: Nijar: ECOWAS za ta tattauna da sojoji

Wannan sanarwa dai ta nuna bacin ran gwamnatin juyin mulkin Nijar din a fili, kan abin da suka kira da bai wa tsofaffin jami'an gwamnatin da sojojin suka kifar kima fiye da hukumomin juyin mulkin da ECOWAs ko CEDEAO din ke yi.  Ana dai ganin hakan zai kawo cikas ga duk wani yunkurin tataunawa tsakanin Nijar da kungiyar ta ECOWAs ko CEDEAO, yayin da a hannu guda kuma ya shafi dadaddiyar dangantaka mai tarihi tsakanin makwabciyar kasa Najeriya da kuma Jamhuriyar ta Nijar.

Najeriya | Abuja | ECOWAS | CEDEAO | Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya kana shugaban kungiyar ECOWAS ko CEDEAO Bola Ahmed TinubuHoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

Tun kafin wannan sanarwa ta gwamnatin juyin mulkin sojan Nijar din, al'ummar kasar da dama sun soki matakin na ECOWAS ko CEDEAO da ma makwabciyar kasa Tarayyar Najeriya. A nasa bangare Oumarou Souley na kungiyar farar hula ta FCR masu fafutukar kare hakin dan Adam da ci-gaban dimukuradiyya, yana ganin lalle ya kyautu sojojin da suke mulki su yi hattara wajen kaucewa yanayi na mayar da martani ga kowa domin gudun bata lokaci ba tare da sun yi wa al'umma abin da suke bukata ba.

Karin Bayani: Nijar: Ziyarar jami'an gwamnatin Rasha

Tuni dai wasu 'yan Nijar din suka soma nuna kowasawarsu da ire-iren wadannan sanarwa, inda suke ganin yadda ECOWAS ko CEDEAO da ma kasashe kamar Faransa ke daukar wadannan matakai ba sanarwa ce abin yi daukar kwakkwaran matakai ne mafita. A hannu guda kuma wasu 'yan kasar na jiran ganin matakin da hukumomin Nijar da Najeriyar za su dauka, domin kaucewa tashin-tashinar da daga baya duka bangarorin biyu ka iya yin nadama a kanta ganin yadda kasashen ke hade tsawon lokaci.