1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya: Rikicin ASUU da gwamnati, tura ta kai bango

Ubale Musa AMA(AS)
April 27, 2022

Gwamnati ta dakatar da biyan malaman jami'o'in Najeriya albashi, a wani mataki na martani kan dogon yajin aikin da kungiyar ASUU ke ci gaba da yi a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/4AWY7
Babbar kofar shiga jami'ar Bayero da ke Kano Najeriya
Babbar kofar shiga jami'ar Bayero da ke Kano NajeriyaHoto: Aminu Abubakar/AFP/GettyImages

Ma'aikatar kwadagon Najeriya ta ce bata da wani zabi face tsaida albashin malaman har ya zuwa lokacin da suka janye yajin aikin. Chris Ngige ministan kwadagon kasar ne yace gwamnatin Najeriya ta bi doka wajen daukar sabon matakin da ke iya kara dagula lamura tsakanin gwamnati da malaman jami'o'in na Najeriya. "Sashe na 43 na dokar yajin aiki, dama kudurin babbar kungiyar kwadago ta duniya ILO, sun bai wa mai daukar aiki damar rike albashin ma'aikacin dake yajin aiki a lokacin da ma'aikacin ke yajin aiki. Dokar ta tanadi amfani da wannan albashi idan ana son maye gurbin aiyyukan masu yajin aikin."

Ministan kwadagon Najeriya ya kuma ce "a wasu kasashen duniya kungiyar masu yajin aikin ce da kanta, kan tanadi kudade biyan albashin 'ya 'yanta a lokacin da suke yajin aikin domin sun san mai daukar aikin ba zai biya wannan albashi ba. Wannan ita ce dokar kuma an yi ta ne da nufin kare tsarin aiki daga rushewa ta yadda in an gama yajin aikin, ma'aikaci na iya samun wurin komawa aikin nasa."

Dakin daukar karatu na wata jami'a a Najeriya
Dakin daukar karatu na wata jami'a a NajeriyaHoto: Olisa Chukwumah/DW

Karin Bayani: ASUU zai ci gaba kauracewa jami'o'in Najeriya

Kokarin bin doka ko kuma kokarin jefa yunwa da nufin murde wuyan malaman makarantar da ke yajin aikin dai, wannan ne karo na biyu a tarihi da gwamnatin Abujar ke amfani da dokar a cikin shekaru biyu. Kuma da kyar da gumin goshi ne ma shugaban kasar, ya amince a biya 'ya 'yan ASUU da suka fada yajin aikinwattani tara shekaru biyun da suka gabata. Ana kallon janye albashin a matsayin jefa malaman a cikin kuncin rayuwa, da kuma ka iya kaiwa ga damuwa duba da yadda wasu ke rayuwa hannu baka hannu akushi.

Ministan kwadagon Najeriya ya ce "Matakin da gwamnati ta dauka, ba yana nufin da cewa ba ma son tattaunawa da 'ya 'yan kungiyar ASUU ba ne, amma muna bin dokar da majalisar tarrayar Najeriya ta kafa ne, ba wai dokar Ngige ko Shugaba Buhari ba, ko kuma Jonathan. Kuma kungiyar ILO ta kalle ta, ta ga kuma ko kadan bata da illa kuma kasashe 187 na kungiyar ILO ne sun kafa wannan doka."

Karin Bayani: ASUU ta shiga sabon yajin aiki

Wasu daliban jami'ar Lagos
Wasu daliban jami'ar LagosHoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

To sai dai kuma a fadar Farfesa Abdulkadir Mohammed dake zaman babban jami'i a kungiyar ASUU a reshenta na jihar Kano, sabon matakin gwamnatin ba zai iya karya gwiwar malaman dake neman gyara ba.

"Tun kafin mu shiga wannan yajin aiki ai yana daya daga cikin abun da muka yi tunanin gwamnati za ta yi, saboda sun saba ba yau suka fara ba. Suma 'ya 'yanmu suna sane saboda haka sun yi tanadi wani dan abun yi da za su rike kansu da iyalansu kafin zuwa kare yajin aikin. Abun da muka sani shi ne wannan tsari na hukumci da yunwa bai taba yin tasiri ba kuma awannan lokaci ba zai yi wani tasiri ba, kuma in bai tasiri ba suna iya tunanin korarmu daga aiki, shi ma wannan ba zai yi tasiri ba."

Abin jira a gani shi ne irin yadda yadda sabon matakin zai kasance a cigaba da takaddamar da ake tsakanin gwamnatin da malaman na jami'o'in Najeriya.