1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yajin aikin ASUU ya tayar da kura

Uwais Abubakar Idris RGB
February 14, 2022

Kungiyar Malaman jami'o’i ta Najeriya ta sanar da shiga yajin aiki na wata guda. ASUU ta zargi gwamnati da gazawa a cika alkawuran da ta yi wa kungiyar.

https://p.dw.com/p/470cW
Protestierende Studenten während ASUU Streik in Kano
Hoto: DW/N. S. Zango

Kungiyar Malaman jamio’i ta Najeriya wato ASUU ta sanar da fara yajin aiki na gama gari na tsawon wata guda, yajin aikin da ta kira da na gargadi bisa zargin gazawar gwamnati a cika alkawuran da ta yi wa kungiyar na samar da kudadden gudanarwa ga jami’oin na gwamnati.

A wannan Litinin kungiyar ta soma yajin aikin. Tsunduma yajin aikin na tsawon makwani hudu da kungiyar malaman jamio’in ta ayana ya kawo karshen zaman tsammani cike da fargaba da aka dade ana yi a kan barazanar da kungiyar ta yi, abin da tuni ya shafi harkar ilimin jamio’i da ke karkashin gwamnatin Najeriyar. Dr Chris Piwuna shi ne mataimakin shugaban kungiyar malaman jamio’i ta kasar...

''Gwamnati ba ta cika alkawarin da suka yi mana ba, mun rubuta masu takarda, mun zauna da su amma kowane lokaci suna cewa za su yi, wannan ya sa muka sake komawa yajin aikin da muka dakatar''

Nigeria Bayero Universität in Kano
Kofar Jami'ar Bayero da ke Kanon NajeriyaHoto: Aminu Abubakar/AFP/GettyImages

Yajin aiki a tsakanin malaman jami'o’in gwamnatin Najeriya, kusan ya zama dan kullum, domin a shekarar 2020 sai da suka kwashe watani tara suna yajin aiki, duka a kan abu guda na zargin gwamnati a gaza cika alkawarin da ta yi ma malaman na samar da kudadden gudanar da jami'o’in.

Malaman sun dage a kan an saba masu kama daga kudadden alawus alawus, ya zuwa ga na gudanar da jami'o’in, amma ga Malam Abdulkareem Garba masani a fanin ilimin boko, na bayyana illar yajin aiki ga karatun jami’a. ''Illolin sune, yara ba sa iya kamalla karatunsu a lokacin da ya dace kuma Idan aka yi rashin sa’a yaro ya koma gida sai ya hadu da wasu miyagun abokai, sannan iyaye suna cikin kunci, kudadden makarantan da za su biya a cikin shekaru hudu sai su kai shekaru bakwai’’ 

Har ya zuwa yanzu, gwamnatin ba ta ce uffan ba a kan wannan yajin aikin ASUU na gargadi, domin ta dage kan cewa tana iyakar kokarinta a kan wannan batu da ya kai wa kowa a wuya, musamman yaran marasa galihu da suka dogara ga jami'o’in gwamnati a kasar. Daka yajin da malaman jami'o’in Najeriyar suka yi suka sha ya tunzura dalibai da iyayensu, domin har yanzu ba su kai ga farfadowa daga koma bayan da karatun boko ya fuskanta ba, a dalilin bullar annobar Corona.