1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Likitocin Najeriya sun amince da komawa bakin aiki

Uwais Abubakar Idris MAB
October 4, 2021

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ta dakatar da yajin aikin da 'ya'yanta suka kwashe watanni biyu suna yi, abin da ya haifar da farin cikin al''umma saboda matukar wahalhalun da suka samu kansu a ciki.

https://p.dw.com/p/41Eoz
Nigeria Selbstmordanschlag in Konduga Verlezte im Krankenhaus von Maiduguri
Hoto: Reuters

Murna da farin ciki sun barke tsakanin mafi yawan ‘yan Najeriya bayan samun labarin janye yajin aikin na likitoci masu kwarewa da ya kai wa kowa iya wuya suka yi, musamman ma dai masu karamin karfi da suka dogara da asibitocin gwamnati domin a kula da lafiyarsu. Sai da ta kai ga likitocin masu neman kwarewa ga jefa kuri'a a taron da suka kwashe daren Lahadi suna yi kafin janye yajin aikin, inda likitoci 56 suka jefa kuri'ar amincewa a janye yajin aikin, abin da ya sanya suka rinjayi 28 daga cikinsu, a cewar Dr Godiya Ishaya, shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya.

Sai dai likitocin sun dakatar da yajin aikin na tsawon makonni shida ne don ba da dama ga gwamnati ta biya masu bukatunsu. Kwanaki 63 suka kwashe suna yajin aikin da ta kai ga babbar kungiyar likitoci ta kasar sanya baki da ma rokon su da su bari haka, a yanayi na rarrashin su. 

Verletzte nach dem Anschlag in Potiskum Nigeria 10.11.2014
Marasa lafiya sun tagayyara sakamakon rashin likitoci a NajeriyaHoto: picture-alliance/Ap Photo/A. Adamu

Yanzu da suka sanya wa'adi na makonni shida ko wannan na nufin za su sake komawa Kenan in ba a biya masu bukatunsu ba? Dr Godiya Ishaya, shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ya ce za su yi nazari don ganin ko gwamnati ta biya musu bukatunsu don yanke shawara.

Sai dai kwararru na bayyana bukatar gwamnatin Najeriya ta dauki mataki na kawo karshen yaje-yajen aiki a kasar musamman na ma'aikatan kula da lafiya da ke kara jefa marasa karfi cikin wahalhalu.