1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka da China sun shiga yakin tattalin arziki

Matthias von Hein ZMA
November 15, 2023

Takaddamar a kan tattalin arziki da ake yi tsakanin Amirka da China ya jefa Jamus cikin wadi na-tsaka-mai wuya kasancewar, Amurka ce babbar aminiyarta,sa'an nan tana yin huldar kasuwanci da China.

https://p.dw.com/p/4YqNN
 Joe Biden da Xi Jinping
Joe Biden da Xi JinpingHoto: Saul Loeb/AFP/Getty Images

Ana iya cewar dangantakar da ke tsakanin  Amurka da China ba ta wani abun azo a gani ba ne. An kusan samun arangaman jiragen saman sojin kasashen biyu  a kan tekun kudancin China. Sannu a hankali takunkumin fitar da kayayyaki na karuwa tare da rikidewa zuwa yakin tattalin arziki. Sa'an nan kuma Beijing ta janye jakadun zaman lafiya uku  Tian Tian, Mei Xiang da Xiao Qi daga Washington.

Fatan kasashe na warware rikicin tsakanin Amirka da China

Shugaban kasar China Xi Jinping
Shugaban kasar China Xi Jinping Hoto: Huang Jingwen/Xinhua/picture alliance

  Babban dalilin da ya sa ke'nan tsawon shekara guda duniya ta ke dakon ganawar farko ta keke da keke tsakanin shugaban kasar China kuma shugaban jam'iyyar da ke mulki Xi Jinping da shugaban Amurka Joe Biden a birnin San Francisco. Ko da dai ba a tsammanin taron kolin na kasa da kasa ya haifar da wani gagarumin sakamako, kamar yadda masanin kimiyyar siyasa na Berlin- Hanns Maull nunar a wata hira da yayi da tashar DW: Ya ce "A yanzu haka muna ganin an koma tattaunawa ne kawai, amma hakan bai ce komai ba game da ko za a iya tinkarar musabbabin rashin jituwar da ke tsakanin Amurka da kasar China, kuma akwai batutuwan da suka shafi rikice-rikice masu tsanani, da kuma ko za a samu ci gaba dangane da warware wadannan matsaloli ta hanyar tattaunawa a wannan taron ba. mafi yawan masu lura da al'amura na shakkar hakan, kuma ni ma zan yarda da hakan".

Ba a tsammanin taron kolin na kasa da kasa ya haifar da wani gagarumin sakamako

Indonesien Bali G20-Gipfel | Treffen Xi Jinping, Präsident China & Joe Biden, Präsident USA
Hoto: Saul Loeb/AFP/Getty Images

Babban dalilin da ya sa ke'nan tsawon shekara guda duniya ta ke dakon ganawar farko ta keke da keke tsakanin shugaban kasar China kuma shugaban jam'iyyar da ke mulki Xi Jinping da shugaban Amurka Joe Biden a birnin San Francisco.  Ko da dai ba a tsammanin taron kolin na kasa da kasa ya haifar da wani gagarumin sakamako, kamar yadda masanin kimiyyar siyasa na Berlin Hanns Maull nunar a wata hira da yayi da tashar DW:
 

Jamus cikin halin tsaka mai wuya saboda rikicin Amirka da China

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Chris Emil Janssen/IMAGO

Wannan kuma na faruwa ne saboda yawancin samfuran kayan da ake sarrafawa da ke da nasaba da kare yanayi da sabunta makamashi na da lakabin kasar China a kansu, hakan ne kuma ya jefa Jamus cikin wadi na tsaka mai wuya a cewar Josef Braml: Ya ce "Ya shafi Jamus sosai. A gefe daya Berlin ta dogara sosai ga Amurka kuma ta ba da tsaronta ga babban kwamandan Washington, wanda zai iya sake zama Donald Trump. A daya hannun kuma, ta na dogara ne kan kasar China idan ana maganar sabbin makamashi. Mun gudanar da bincike da ke nuni da cewar, mun yi watsi da albarkatun mai, mun rufe tashoshin nukiliya, kuma muna son sabbin hanyoyin samun makamashi, don haka mun dogara sosai kan kasar  China.

Rikicin tattalin arzikin na kasashen ya shafi ma Turai

Frankreich, Straßburg | Flaggen vor dem Europarat
Hoto: Patrick Hertzog/AFP/Getty Images

 Manazartan dai sun kwatanta matakin daidaita al'amuran Jamus tsakanin Beijing da Washington a matsayin "mai matukar kalubale". Duk da haka, Maull, wanda shi ne babban jami'in harkokin kasuwanci a Berlin, yana mai ra'ayin cewar wannan yanayi bai shafi Jamus ita kadai ba. Suma saboda Tarayyar Turai ta kasance mai taka muhimmiyar rawa a fagen huldar tattalin arzikin kasa da kasa, "Jamus tana da nauyi a matsayin wani bangare na EU kuma tana da wani tasiri a kan Amurka.