1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirkar ta saki fursunonin Iran

Abdourahamane Hassane
September 19, 2023

Tsofaffin fursunonin Amirka a Iran da suka hada da wanda aka daure shekaru takwas a gidan yari, da wasu 'yan gidansu biyu,

https://p.dw.com/p/4WV5m
Hoto: Qatar News Agency/UPI Photo/Newscom/picture alliance

Fursunonin sun tashi daga birnin Tehrana cikin jirgin saman Qatar Airways zuwa Doha inda suka tsaya, kafin su sake tashi domin isa Amirka. A ranar Litinin(18-9-23) ne Amirka da Iran din suka gudanar da musayar fursunoni a karkashin wata yarjejeniya da ta hada da mikawa Iran  kudadensu da aka rike  dala biliyan 6, yayin da kuma  Amirkar ta saki fursunoninIran  guda biyar. Kasar Qatar na daya daga cikin kasashen da suka shiga tsakani aka cimma yarjejeniyar.