1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsige kakakin majalisar dokokin Amirka

Suleiman Babayo USU
October 4, 2023

A karon farko cikin tarihin kasar Amirka an tsige kakakin majalisra dokokin kasar Kevin McCarthy na jam'iyyar Republican mai rinjaye a majalisar.

https://p.dw.com/p/4X5Y3
Amirka | Majalisar wakilai | Kevin McCarthy kakakin majalisar dokokin Amirka da aka tsige
Kevin McCarthy kakakin majalisar dokokin Amirka da aka tsigeHoto: J. Scott Applewhite/AP/picture alliance

'Yan majalisar dokokin Amirka sun kada kuri'ar tsige kakakin majalisar, Kevin McCarthy a wani mataki da ke zama na farko a tarihin kasar. 'Yan majalisa masu matsanancin ra'ayi na jam'iyyar Republican da ke da rinjaye suka kawo karshen mulkin kakakin, abin da ya jefa shugabannin jam'iyyar mai adawa a kasar cikin rudani.

McCarthy ya shaida 'yan majalisa cewa ba zai sake tsayawa takara kan sake neman mukamun ba. Matakin zai tsayar da aikin majalisra dokokin kasar ta Amirka har zuwa makon gobe da ake sa ran samun sabon kakakin majalisar dokokin.