1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Makomar sojojin Amurka a Yamai

Gazali Abdou Tasawa LMJ
September 8, 2023

Matakin Amurka na shirin kwashe sojojinta daga sansaninsu na birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar zuwa cibiyarsu ta biyu a Agadez, ya soma haifar da muhawara a game da manufar da ke tattare da wannan mataki.

https://p.dw.com/p/4W7US
Nijar | Sojoji | Amurka | Horo | Yamai | Agadez | Juyin Mulki
A baya dai sojojin Amurka na bai wa takwarorinsu na Nijar horo kan yakar 'yan ta'addaHoto: DW/A. M. Amadou

A yayin da wasu ke fassara matakin Amurkan na kwashe sojojinta da wasu ma'aikatanta daga sansaninsu na Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar zuwa sansaninsu na jihar Agadez da alamu na yiwuwar Nijar ta fuskanci wani hari daga sojojin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ko kuma na Faransa, wasu na ganin tana kokarin nisanta sojijin nata ne da sansanin nasu mai makwabtaka da na Faransa a birnin na Yamai.

Karin Bayani: PNDS Tarayya ta yi martani ga firaminista

Ma'aikatar tsaron Amurkan ce dai ta sanar da wannan mataki, makonni shida bayan juyin mulkin da sojoji suka yi. Sai dai Amurkar ta ce babu wata barazana da sojojinta 1,100 ke fuskanta kawo yanzu, kuma matakin ba shi da wata alaka da takun sakar da ake tsakanin Faransa da Nijar din ko kuma Nijar da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO.

Nijar | Sojoji | Amurka | Horo | Yamai | Juyin Mulki | Bazoum Mohammed | Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da Bazoum MohammedHoto: Presidency of Niger/AA/picture alliance

To sai dai tuni 'yan kasar ta Nijar suka soma yi wa matakin fassara dabam-dabam, inda Malam Chayib Mohamed wani matashin dan siyasa mai kusanci da hambararren shugaban kasa Bazoum Mohamed na ganin matakin na alamta kara tabbatar da yiwuwar daukar matakin soja a kan masu juyin mulkin. Sai dai wasu na ganin a nan gaba ne za a iya sanin manufar Amurkawan, amma a yanzu babu wata tsama tsakanin kasashen biyu.

Karin Bayani: Aljeriya: Warware rikicin Nijar ta diflomasiyya

Yanzu haka dai hukumomin kiwon lafiya na kasar Nijar sun soma daukar matakan rigakafin afkuwar hari a birnin Yamai da gargadi kan matakan kariya da jama'a za su iya dauka in an kai harin soja, a yayin da manyan asibitoci na birnin suka fara atisaye na ayyukan ceto da kuma karbar gawarwaki da mutanen da za su jikkata. A hannu guda kuma, suma 'yan sanda masu aikin kula da zirga-zirgar ababen hawa aka mallaka musu bindigogi kirar AK 47.