1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar gwamnati na ci gaba da yin turjiya wa ECOWAS

Uwais Abubakar Idris AH
August 25, 2023

Shugaban kungiyar bunkasa tattalin arziki ta kasashen Afrika ta yamma Ecowas Jamhuriyar Nijar, inda ya ce har yanzu suna kan bakarsu na amfani da matakin sulhu da ma na soja a kan gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar:

https://p.dw.com/p/4VadN
Abdel-Fatau Musah kwamishinan ECOWAS
Abdel-Fatau Musah kwamishinan ECOWASHoto: Francis Kokoroko/REUTERS

Shugaban kungiyar bunkasa tattalin arziki ta kasashen Afrika ta yamma Ecowas ya yi jawabi ga ‘yan jaridu a kan rikicin siyasar Jamhuriyar Nijar, inda yace yanzu suna kan bakarsu ta amfani da matakin sulhi da ma na soja a kan gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar, kuma suna yi hakan ne domin tabbatara da dorewar mulkin dimukurdiyya da ceto halin da alummar kasar ke ciki. Daga Abuja Uwaisu Abubakar Idris ya aiko da wannan rahoto

Karin bayyani.

Shugaban na kungiyar Ecowas Omar Touray da ya kwashe lokaci mai tsawo yana bayani a kan rikicin siyasar Jamhuriyar Nijar da halin da ake ciki yanzu da ma matakan da za su dauka a nan gaba, ya bayyana cewa dukkanin matakan da suka dauka ya zuwa yanzu suna a cikin dokokin kungiyar da dukkanin kasashe ciki har da Nijar din ta amince da su, to sai dai ya ce a yadda al'ammura ke tafiya akwai buktar fahimtara al'ammura domin rarrabe aya da tsakuwa da ma kaucewa rashin fahimtar juna inda ya ce.

‘' Bari in yi maku bayani dala-dala cewa Kungiyar Ecowas ba ta kadammar da yaki a kan al'ummar Jamhuriyar Nijar ba, kuma ba ta niyyar yin haka kamar yadda ake yayatawa. Abin da shugabanin Ecowas suka yi shi ne amfani da dokar da ta ba da ikon sanya takunkumi domin tilasta maido da doka da oda bisa mulkin dimukurdiyya. A yanzu ana kokari na sulhu muna fatan kokari na diplomasiyya zai samar da sakamako, amma kuma za mu ci gaba da aiki na shirya sojojin rundunar ko ta kwana don turasu. Wannan juyin mulki na Nijar abin takaici ne domin ya faru ne a dai-dai lokacin da al'amura ke tafiya dai dai ta fanin tattalin arziki da tsaro.

ECOWAS na kan bakanta na tura sojoji a Nijar domin dawo da Bazoum a kan mulki

 Abdourahamane Tiani shugaban mulkin sojin Nijar
Abdourahamane Tiani shugaban mulkin sojin NijarHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

A dai-dai lokacin da Kungiyar ta Ecowas ke dagewa a kan maido da dimukurdiyya a Jamhuriyar Nijar, tare da watsi da gwamnatin rikon kwarya da ta ba da wa'adin mulki na shekaru uku.Kungiyar ta ce juyin mulki babban koma baya ne ga kokarin da ake a yankin Afrika ta Yamma na karfafa mulkin dimukurdiyya bayan koma bayan da aka samu a shekarun 1990 na juye-juyen mulki da yakin basasa a Liberiya da Saliyo. To sai dai ga Dr Elharun Muhammad shugaban cibiyar ci gaba da tsare-tsare kasa ya ce akwai bukatara yin taka tsan-tsan. A yayin da ake ci gaba da kokari na diplomasiyya a kan wannan batu inda kasashen kungiyar ta Ecowas ke jan daga a kan gwamnatin mulkin sojin Nijar din da ke turjewa, Juyin mulkin da aka yi a Jamhutiyar Nijar da it ace kasa ta hudu a yankin a yanzu da ya nuna barazana ta sake yin katsalandan na sojoji a dimukurdiyya na zama babban barazana ga sauran kasashen yankin. Wannan  ya kara jefa kasashen yankin ciki hali na kiki-kaka a fanin tsaro, tattalin arziki da  zamantakewar al'ummarsu.