1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta saka sojoji cikin shirin yaki

Ubale Musa SB/ATB
August 10, 2023

A ci gaba da kokarin tilasta sojan Jamhuriyar Nijar ajiye mulkin kasar, shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS sun nemi saka rundunar tsaron ko-ta-kwanan yankin cikin shiri bisa makomar kasar Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/4V1A3
Najeriya, birnin Abuja | Taron Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEOA
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEOAHoto: Gbemiga Olamikan/AP/picture alliance

Duk da cewar dai basu kai ga fitowa fili su ambaci karfi na hatsi ba, daga dukka na alamu hakuri na kasashen ECOWAS na dada raguwa bisa tsaiwa irin ta gwamen jakin sojan Jamhuriyar Nijar da suka kwace madafun iko. Wani taro na kasashen da akak kammala da yammaciyar yau din nan dai ya nemi rundunar ko ta kwanan yakin da su kasance cikin shirin abkawa Jamhuriyar Nijar har aka kasa cimma daidaito a tsakanin kasashen da sojan da ke dada baza fukafukin zama a daukacin kasar.

Karin Bayani: Nijar: Bukatar tabbatar da zaman lafiya

Jamhuriyar Nijar, Yamai | Janar Mohamed Toumba  dna sojojin da suka yi juyin mulki
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Sanarwar bayan taron dai ta yi Allah wadarai da ci gaba da garkuwa da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, ko bayan kunnen uwar shegu da bukatar tattaunawa da kasashen yankin. Sanarwar da shugaban hukuma ta gudanarwar ECOWAS Dr Omar Alieu Touray ya karanta dai ta ce kasashen sun nemi sanya sojoji cikin shirin ko-ta-kwana.

ECOWAS a fadar Tourey za ta ci gaba da daukacin takunkumin da ke kan Jamhuriyar Nijar bayan gargadi ga kasashen yankin da ke tarnaki ga matakin kasashen yankin, ECOWAS za ta ci gaba da tabbatar da takunkumin da ke kan Jamhuriyar Nijar da suka hada da rufe iyaka da hana zurga-zurga, da ma kwace kaddarorin sojojin da suka yi juyin mulki.

Ko bayan nan kuma kasashen yankin za su kwace dukiya da kaddamar da takunkumi ga kungiyoyi da mutanen da aiyyukansu ke barazana ga kokarin sake mai da demokaradiyya a cikin Niger. Haka kuma ECOWAS na gargadin kasashen da ke goyon bayan sojojin da suka kifar da gwamnatin Jamhuriyar Nijar kan irin girman hukuncin da suke iya fuskanta bisa matakinsu.

Najeriya, birnin  Abuja | Lokacin taron kungiyar  ECOWAS
Shugaba Evariste Ndayishimiye na Burundi a tsakiya da Omar Toura shugaban hukumar ECOWAS a hannu gami da Adamu Ibrahim Lamuwa na ma'aikatar harkokin wajen NajeriyaHoto: KOLA SULAIMON/AFP

ECOWAS tana kuma nemi kungiyar Tarrayar Afirka dat a aiwatar da duk matakan ECOWAS Jamhuriyar Nijar. Sannan kuma da kawaye na kasashen ECOWAS na kuma neman daukacin kawayen yankin da suka hada da majalisar dinke duniya a kokarinta na sake mai da demokaradiyyar Niger a cikin sauri.

Kasashen yankin sun kuma nemi shugaban hukuma ta gunawar yankin da ya lura da aiwatar da daukaci na takunkumi na kasashen. Sannan kuma sun umarcvi hafsoshi na kasashen yankin da su sanya rundunar tsaron ko ta kwanan yankin da su kasance cikin shirin ko ta kwana da nufin sake mai da kasra ta Jamhuriyar Nijar bisa tsarin mulki. A yayin da alal ga misali kasashe irin Cote d'Ivoire renon Faransa ba zabi face mai da Mohamed Bazoum bisa mulki ko ta halin kaka, ga Najeriya da ke tsaka cikin siyasa ta gida har yanzu akwai damar sulhu.