1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin PNDS ga firaministan Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
September 5, 2023

'Ya'yan jam'iyyar PNDS Tarayya a Jamhuriyar Nijar da magoya bayansu, sun fara mayar da martani ga bayanan firaministan gwamnatin juyin mulkin kasar Ali Lamine Zaine kan tattaunawa da ECOWAS da binciken tsohuwar gwamnati.

https://p.dw.com/p/4VzNm
Nijar | Sojoji | Juyin Mulki | Firaminsta | Ali Mahaman Lamine Zeine | PNDS | Martani
Sabon firaministan gwamnatin juyin mulkin sojan Nijar, Ali Mahaman Lamine ZeineHoto: DW

Firaministan gwamnatin juyin mulkin sojan ta Jamhuriyar Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine  ya kuma yi bitar jerin matsalolin da yace gwamnatocin PNDS Tarayyar sun haddasa wa kasar, a cikin sama da shekaru 12 na mulkinsu da suka hada da ciyo bashin da ya wuce kima. Guda daga cikin batutuwan da suka fi jan hankalin wasu 'yan jamiyyar ta PNDS Tarayya shi ne, batun bashin na miliyan 5000 da 200 da ya ce gwamnatin jamhuriya ta bakwai ta ciyo. Da yake mayar da martani kan wannan batu, Malam Sahanin Mahamadou daya daga cikin matasan jam'iyyar ta PNDS Tarayya ya ce firamnistan bai fadi gaskiya dangane da wannan al'amarin ba. Firamnistan na Nijar dai ya ce gwamnatinsa za ta gudanar da bincike kan yadda gwamnatocin jamhuriya ta bakwai suka tafiyar da aiki, kana su mika wa kotu duk takardun binciken almundahana da ake zargin an aikata a tsawon shekaru 12.

Nijar | Sojoji | Juyin Mulki | Bazoum Mohamed | PNDS
Hambararren shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Bazoum MohamedHoto: Gazali A. Tassawa/DW

Dangane da wannan batu Malam Chayib Mohamed shi ma matashi a jam'iyyar ta PNDS Tarayya kana mai kusanci da shugaba Bazoum Mohamed ya ce, ba sa tsoron binciken  da ba mamaki  allura ta tono garma. Wani batun na dabam da Firamnista Ali Zeine ya ambato shi ne cika duk sharuddan da kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO ta gindayawa gwamnatinsu, inda ya ce abin da ya yi saura shi ne zama da kungiyar a nan gaba domin cire wa kasar takunkumi. To sai dai Malam Lawal sallaou Tsyabaou shugaban kungiyar RODAHD mai kusanci da tsohuwar gwamnati, ya ce batun bah aka yake ba. Firamnistan na Nijar dai ya ce duk da takun-sakar da kasar ke yi da Faransa kan batun zaman jakada da ma sojojin Faransan, ba su da niyyar kutsa kai ofishin jakadancin Paris din domin tisa keyar jakadan zuwa kasarsa. A cewarsa yin hakan ya saba da doka, kuma su suna son kiyaye dokokin kasa da kasa kamar yadda suka yi alkawari tun da farko.