1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Zargin musayar makamai tsakanin Putin da Kim Jong Un

October 7, 2023

Karuwar zirgar jiragen kasa a iyakokin Rasha da Koriya ta Arewa ta saka fargabar yiwuwar musayar makamai tsakanin kasashen biyu abokai da ke takun saka da kasashen Yamma.

https://p.dw.com/p/4XEaF
Fargabar musayar makamai tsakanin Rasha da Koriya ta ArewaHoto: Mikhail Metzel/Russian President Press Office/dpa/picture alliance

Wani bincike da cibiyar nazarin badarun kasa da kasa ta Amurka ta gudanar ya nunar de cewa zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Koriya ta Arewa da Rasha ta karu sosai a 'yan makonnin nan, lamarin da ke nuni a kwai yiwuwar kasashen biyu na yin musayar makamai a tsakaninsu.

Karin bayani: Ziyarar Kim ga Putin ta sa Amurka fargaba

A dai samu karuwar jirga-zirgar jiragen kasa a iyakokin Rasha da Koriya ta Arewar ne bayan ganawar da shugaba Kim Jong Un ya yi da takwaransa Vladimir Putin a yayin ziyarar da ya kai Rasha a watan jiya.

Karin bayani: Kim Jong Un ya isa kasar Rasha

Kasashen biyu dai na karkashin takunkuman kasa da kasa wadanda aka kakaba wa Moscow saboda mamayewar da ta yi wa Ukraine ita kuwa Pyongyang saboda shirinta na nukiliya.

Tuni dai Amurka ta yi martani kan wannan batu tana mai cewa musayar makamai tsakanin Koriya ta Arewa da Rasha a cikin wannan yanayi ya saba wa kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wadanda ita da kanta Rashar ta kada kuri'a amincewa da su.