1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Kim Jong Un ya isa kasar Rasha

September 12, 2023

Shugaban Koriya ta Arewa ya isa kasar Rasha, a ziyararsa ta farko zuwa kasar ketare tun bayan bullar cutar Corona da ta addabi duniya a shekaru uku da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4WECm
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong UnHoto: Korean Central News Agency/Korea News Service/AP/picture alliance

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya isa Rasha a wannan Talata, inda ake sa ran ganawa a tsakaninsa da Shugaba Vladimir Putin a Rashar.

Ma'aikatar tsaron Koriya ta Arewa ce ta ba da labarin isar shugaban kasar a Rashaa wannan safiya, bayan tafiyar da ya yi da wani jirgin kasa mai sulke na kashin kansa.

Ita ma rundunar soja ta kasar Koriya ta Kudu da wasu kafafen watsa labarai a Rasha, duk sun tabbatar da shigar Shugaba Kim Jong Un cikin Rashar da safiyar wannan Talata bayan barin kasarsa a ranar Lahadi.

Masu fashin baki dai na ganin La-budda, Shugaba Putin na Rasha zai bukaci manyan makaman Atilare da wasu masu karfin kakkabe makamai masu linzami daga Koriya ta Arewar.

Ana kuma sa ran shugabannin biyu, za su tattauna ne a birnin Vladivostok na Rasha.