1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Taliban ta haramta wa mata zuwa makaranta a Afghanistan

March 20, 2024

An bude makarantu a Afganistan don gudanar da sabon zangon karatu amma ba tare da 'ya'ya mata ba, kusan shekaru uku kenan a jere da ake haramta wa mata zuwa makaranta tun bayan kafa gwamnatin Taliban.

https://p.dw.com/p/4dvAT
Zuhal Hakimi, dalibar karshe dake karantar ilmin aikin kiwon lafiya da Taliban ta kora.
Zuhal Hakimi, dalibar karshe dake karantar ilmin aikin kiwon lafiya da Taliban ta kora. Hoto: privat

Taliban dai ta haramta wa mata zuwa makaranta a watan Maris din 2022, tun bayan da ta hambarar da gwamnatin Kabul da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya. Su ma dai jami'o'in gwamnati da suka fara sabuwar shekarar karatu sun hana mata shiga aji tun watan Disambar 2022.

karin bayani: Koma bayan Iimi a Afganistan 

Gwamnatin Taliban ta sanya Shari'ar addinin Musulunci a Afghanistan, wace ta fi dakile hakkokin mata a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

A jiya talata 19 ga watan Maris 2024, hukumomin kasar suka fito da jadawalin karatun shekarar nan da muke ciki a wani dan kwarya-kwaryar biki da suka shirya a birnin Kabul ba tare da wakilcin 'yan jarida mata ba, inda aka haramta musu daukar rahoto a wajen taron.

karin bayani: Taliban: Mata za su koma karatun boko