1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsawaita aiki MDD a Afganistan

Zainab Mohammed Abubakar
September 17, 2021

Kwamitin sulhu na MDD ya amince da tsawaita ayyukan rundunar majalisar da ke Afghanistan da karin watanni shida, tare da bukatar Taliban ta kafa gwamnati mai wakilcin mata.

https://p.dw.com/p/40TgR
Ghosts of Afghanistan
Hoto: Java Films

Baki dayansu ne dai, wakilan kwamitin 15 suka amince da tsawaita aikin siyasa na UNAMA, tawagar da ke lura da batutuwan raya cigaban kasar da wasu batutuwa amma ban da zaman lafiya.

Kudurin dokar ya jaddada muhimmancin sanya wakilai cikin gwamnati, duk da cewar tuni 'yan Taliban din suka kafa gwamnatin da ta kunshi wakilansu kadai, kuma babu mace ko da guda daya.

Bugu da kari dokar ta nemi bai wa mata 'yancin shiga harkokin kasa, tare da kare hakkin al'umma ciki har da na mata da yara da daidaikun cikinsu marasa rinjaye.