1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koma bayan iIimi a Afganistan

Usman Shehu Usman
December 6, 2023

A kasar Afganistan samari na fiskantar koma bayan karatu baya ga 'yan mata da a baya suka rasa damar karatu musamman bayan da mayakan Taliban suka karbi iko kasar

https://p.dw.com/p/4ZqDL
Sacharow-Preis 2023 Kandidaten/Matiullah Wesa
Hoto: Sanaullah Seiam/AFP/Getty Images

A cewar kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch, matasa da dama za su rasa damar yin karatu a bisa sabon tsarin karatun da jadawalin karatun da gwamnatin Afganistan ta fitar. Babbar matsalar dai ita ce hana mata malamai shiga azuzuwa, wannan babbar barazana ce ga fannin ilimin boko, domin a baya ana da malaman makaranta mata da yawa, yanzu kuma kafin a samu maza da za su maye gurbinsu zai kasance babbar matsala. Wata babbar matsalar ita ce akasarin matasa suna tafiyar neman kudi domin ciyar da iyayansu, maimakon zuwa makaranta, wannan kuwa ya yi matukar karuwa tsakanin iyalai domin idan aka yi la'akari da yadda kasar ke fiskantar rushewar tattalin arziki, wanda ke tilastawa iyalai tafiyar neman abun sawa a baka a madadin tura 'ya'yansu izuwa azuzuwa don neman ilimi.