1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar sauya sheka a Tarayyar Najeriya

January 11, 2024

Wani abu da ke kama da yunkuri na rushe adawa a Najeriya, ana ci gaba da ganin tururuwar masu adawa zuwa ga jam'iyyar APC mai mulki cikin kasar, abin kuma da ke janyo sharhi sosai.

https://p.dw.com/p/4b82z
Shugaba Bola Tinubu da madugun adawa Atiku Abubakar

A cikin tarihi na siyasar Najeriya dai, lokaci na kammala shari'un zabe na zaman mafi wahala ga masu adawa ta kasar.

An dai sha kallon kokari na sauyin sheka a bangare na masu adawar, ko dai a kokari na kauce wa ‘yunwa ko kuma rikicin cikin gida mai zafi. To sai dai kuma wata ziyarar kakaki ga dantakara na jam'iyyar PDP ta adawa a zaben shugaban kasar da ya gabata dai, na jawo dagun hakarkari a fagen siyasar Najeriyar a halin yanzu.

Bayan ziyarar da ya kai fadar gwamnatin kasar a Abuja, Daniel Bwala da ya jagoranci fada a kokari na dora Atiku bisa mulki, ya ce kasar ta dade ba ta ga shugaban da ke ta kokarin ceton lamura ba kamar Bola Tinubu. Daniel Bwalan da a baya ya kira shugaban da kalamai da ke da kamar wuya a maimaita su dai ya yi tsallen badake tare da nesanta kansa cikin rawar da ya taka a lokacin yakin neman zabe.

Kokarin warware matsalar cikin kasa ko kuma neman kare matsalar aljihu dai, Bwalan na zaman na baya-baya cikin jerin masu adawar da yanzu haka APC mai mulkin kasar ke yi wa karatun mesa. Ana dai kallon maimata salo irin na jam'iyyar PDP da a baya ta hadiye duk wani mai takama da adawa cikin kasar amma kuma ta kare a cikin mummunan rikicin cikin gidan da ya kare burinta na kaiwa 60 bisa mulki.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed TinubuHoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Ibrahim Abdullahi dai na zaman mataimaki na kakakin PDP na kasa, kuma ya ce sun hango ‘yar gidan jiya a bangaren APC mai hadiya amma kuma ba ta da hanyar ta kasayar da rubabbun yaya.

Ko ma ya zuwa ina masu tsintsiyar ke shirin su kai a kokarin kara yawan magoya bayan dai, sabon matakin dai a tunanin Abdullahi Tanko, jigo a cikin jam'iyyar APC na kama da yabon gwanin da ya zama dole.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin sauyin shekar cikin kasar da ke da bukata ga adawa a kokari na inganta lamura da kila ma kare zarmiya ta masu mulki a kasar.