1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan jam'iyyun Najeriya na rasa 'ya'yansu

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
June 24, 2022

Manyan jam'iyyun siyasar Najeriya na APC mai mulki da PDP ta adawa, na ci gaba da asarar magoya bayansu da ke ficewa daga cikin jam'iyyun musamman a majalisun dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/4DCMC
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Jim kadan bayan kammala zabukan fidda gwani na jam'iyyun siyasar Najeriyar ne dai aka fara fuskantar ‘yayan manyan jam'iyyun suna ta sauya sheka saboda abubuwa na ban mamaki da suka faru. 'Yan siyasa da dama ne suka rasa cin zaben fidda gwanin, abin da ke nuna ba da su za a yi ba a zaben 2023, domin fiye da rabin ‘yan majalisun suna yi wa majalisar da ta tsole masu ido adabo. 

Jamiyyun APC da PDP su ne wannan guguwa ta sauya sheka ta fi kamari a cikinsu. Sanata Abdullahi Adamu, shi ne shugaban jam'iyyar APC mai mulki, kuma da sai da ya kaiga yin takakka zuwa majalisa a kan wannan lamari.

Sabbin jam'iyyu irin na NNPP da Labour da ma SDP su ne kakarsu ta yanke saka domin duk da cewa NNPP sabuwa ce da lilamamin siyasa Dr Rabiu Musa Kwankwaso ke takarar neman shugabancin Najeriya a cikinta, ana mata kallon jam'iyya ta uku mafi karfi a Najeriyar wacce ta kai ga samun wakilci a majalisar datawan Najeriya. 

Bildkombo | Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso und Atiku Abubakar

Duk da cewa ana yi wa wannan sauyi kallon abin da ke sanya manyan jam'iyyun damuwa da makomar da zai iya samarwa, amma ga Barrister Solomon Dalung tsohon ministan matasa da wasanni kuma dan takarar neman gwamnan jihar Plateau a jamiyyar SDP, ya ce abin rawar ‘yan mata ne in an yi gaba sai kuma a koma baya a tsakanin jam'iyyun Najeriyar.

Jamiyyun siyasar Najeriyar na fargabar kalubalen da za su fuskanta saboda masu fitowa fili su sauya sheka da ma wadanda za su iya zama a yanayi na munafuntar jam'iyyusnu musamman a lokacin manyan zabukan da ke tafe, inda ake kokari na kaiwa ga madafun iko na shugabancin kasa ta hanyar dimukuradiyya.