1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janar Tchiani na ziyarar farko a wajen Nijar

Gazali Abdou Tasawa Abdoulaye Mamane (LMJ)
November 23, 2023

Shugaban hukumar mulkin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ya soma wata ziyarar aiki a kasashen Mali da Burkina Faso a karon farko tun bayan kifar da gwamnatin Bazoum

https://p.dw.com/p/4ZMCU
Janar Abdourahamane Tiani, shugaban gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar
Janar Abdourahamane Tiani, shugaban gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar NijarHoto: Télé Sahel/AFP

Shugaban hukumar mulkin sojan kasar Nijar janar Abdourahmane Tchiani ya tashi zuwa kasashen biyu ne na Mali da Burkina Faso tare da rakkiyar wata babbar tawaga wacce ta kunshi ministan biyar da suka hada da ministan tsaro da na harkokin waje da na matasa da raya al'adu da jakadan Nijar a Mali da karamar jakadar Nijar a burkina Faso.

Karin Bayani:  Kotu ta yi watsi da koken Jamhuriyar Nijar

Fadar shugaban hukumar mulkin sojan kasar ta Nijar ba ta yi bayani kan makasudin wannan ziyara da kuma muhimman batutuwa da Janar din zai tattauna da takwarorin nasa a biranen Bamako da Ouagadougou, to amma sai dai wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Mali ta bayyana cewa za a gudanar da taron majalisar ministocin kasashe membobin kungiyar kawance ta AES da suka hada da Mali da Burkina Faso da Nijar a birnin Bamako, kuma wasu shugabannin mulkin sojin kasashen ne za su jagoranci zaman majalisar.

Karin Bayani:  Sojoji a Nijar sun karbe iko da kamfanoni gwamnati

Wannan ziyara na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da sojojin Nijar suka dafa wa takwarorinsu na Mali wajen kwato birnin Kidal daga hannun ‘yan tawaye, wanda wasu masu sharhi kan harkokin siyasa kamar Malam Habila Rabiou, ke ganin batun tattalin arziki zai kasance daga cikin jerin batutuwan da shugabannin kasashen za su mayar da hankali a kai a lokacin wannan ziyara.

Dama zuwa hagun, Shugaban Assimi Goïta, Mali Abdourahamane Tiani, Nijar,da Ibrahim Traoré na Burkina Faso
Dama zuwa hagun, Shugaban Assimi Goïta, Mali Abdourahamane Tiani, Nijar,da Ibrahim Traoré na Burkina FasoHoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da shugaban hukumar mulkin sojan kasar Nijar ya kai a wasu kasashen ketare, tun bayan juyin mulkin inda ya kwashe kusan watanni hudu a fadar shugaban kasa ba tare da iya fita waje ba, abin da wasu ‘yan kasar suka dunga fassarawa da tsoron da yake ji na fuskantar hari daga sojojin ECOWAS ko kuma wani bore na cikin gida.

Karin Bayani: Kasar Togo za ta sasanta Nijar da kungiyar Ecowas

Yanzu dai ‘yan Nijar sun zura ido su ga irin wainar da shugaban majalisar ceton kasar ta Nijar zai tayo a kasashen na Mali da burkina faso, bayan hawan kahon da ya yi na bai wa mardansa kunya dangae da shguban da suka share watanni suna yi masa.