1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan wakilin Jamhuriyar Nijar a MDD

Salissou Boukari SB/MAB
September 24, 2023

A Jamhuriyar Nijar kallo ya koma sama dangane da wanda ya kamata ya yi magana da sunan kasar a babban taron da ke gudana a zauran Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/4Wi4b
Birnin New York na Amirka | Taron Majalisar Dinkin Duniya
Taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na AmirkaHoto: Mary Altaffer/AP/picture alliance

A Jamhuriyar Nijar kallo ya koma sama dangane da wanda ya kamata ya yi magana da sunan kasar a zauran majalisar Dinkin Duniya dangane da taron da ake yi karo na 78 inda baya ga Ministan harkokin wajen kasar ta Jamhuriyar Nijar da hukumomin kasar na mulkin soja suka aika, daga bangare daya kuma ministan harkokin waje na hambararrariyar gwamnatin kasar na ikirarin cewa shi ne wakilin na Nijar.

Karin Bayani: Amfani da diflomasiyya a rikicin Nijar

Birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar | Masu zanga-zanga
Masu zanga-zanga a birnin Yamai na Jamhuriyar NijarHoto: AFP/Getty Images

Wannan lamari dai na halartar kasar ta Nijar a babban taron Majalisar dinkin duniya karo na 78 da ke gudana yanzu haka a birnin New York na kasar Amirka ya haifar da cecekuce mai yawa ganin cewa kasar ta Nijar har yanzu tana zaman tankiya da wasu kasashen ECOWAS da kuma Faransa da ma wasu kasashen Turai wanda suke nuna cewa basu yarda da gamnatin da yanzu take Mulki a kasar ta Nijar ba.

Wani kwamiti da ke fafutikar neman cikekken 'yancin kasar ta Nijar suka fitar da sanarwa inda suka ce suna bibiyar lamarin sau da kafa inda ma suka ce sun gano yadda wata kasa daga cikin kasashen yamma na ruwa da tsaki don ganin wakilin da ba tafi daga nan Nijar bai yi Magana a gaban babban taron ba ganin cewa su ba su yarda da hukumomin da suke mulki a kasar ta Nijar ba.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar, Hassoumi Massoudou lokacin mulkin Mohamed Bazoum
Hassoumi MassoudouHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Da dama ne dai daga bangaran gwamnatin da aka hambare ke fatan ganin wakilin na Nijar da sabin hukumomin na mulkin soja suka aika wato Ministan harkokin wajen kasar ta Nijar Yaou Bakary Sangare, bai samu yin magana ba hasali ma inda suke fatan ganin cewa nasu gwanin ne wato tsohon ministan harkokin wajen kasar ta Nijar Hassoumi Massaoudou ya samu yin Magana. Sai dai wannan lamari za a iya cewa na cike ne da sarkakiya domin kuwa sabin hukumomin na Nijar tun da jimawa sun sanar da soke Paspo na wadannan da suke ikirarin magana da sunan Jamhuriyar Nijar inda ma yanzu wata sabuwar takardar sammaci bta fito a kansu wanda sun ana farko shi ne na tsohon ministan harkokin wajen kasar ta Nijar Hassoumou massaoudou da ma tsohon Firaminista da sauran ministoci da suka gudu daga kasar ta Jamhuriyar Nijar.