1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yarjejeniya musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas.

Mahmud Yaya Azare AH
December 20, 2023

A dai-dai lokacin da kwamatin tsaro na MDD ke shirin kada kuri,ar neman tsagaita wuta kan zirin Gaza don dalilai na agaji,Isra,ila ta sanar da shirinta na cimma sabuwar yarjejeniyar

https://p.dw.com/p/4aPs7
Hoto: YUKI IWAMURA/AFP

Kwamatin sulhu na  MDD na shirin kara zaman kada kuri'a kan wani kudiri da zai bukaci tsagaita wuta kan zirin Gaza, bayan da aka dage kada kuri,ar a ranar Litinin,don kaucewa fuskantar hawa kujerar nakin Amurka,wacce ta nemi da a sake kwaskwarima a sigar kudurin, ta hanyar  maye kalmar tsagaita wuta da kalmar bayar da damar rarraba kayan agajin da ake matuƙar buƙata,lamarin da Amurkan da ke zama kasa daya tilo da ke kafar ungulu a kudare-kudaren da aka yi ta gabatarwa a baya don tsagaita wuta a Gazan ta ce idan har aka yi shi, za ta lamunta da shi.

Isra'ila na fuskantar matsin lamba na kasashen duniya

Weltklimakonferenz der Vereinten Nationen (COP28) in Dubai
Hoto: Henrik Montgomery/TT/IMAGO

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Isra,ilan ke shan matsin lamba daga kasashen duniya kan ta tsagaita wuta a zirin na Gaza,bayan da yawan wadanda suka kwanta dama a cikinsa ya doshi dubu  20,kwanaki 75 bayan da ta kaddamar farmakin daukar fansa kan kungiyar Hamas dat a kai ma ta hare-haren. Kamar yadda Isra,ilan ke fuskantar matsin lamba a cikin gida,daga jam'iyyun adawa da dangin wadanda Hamas ke garkuwa da su,bayan abun kunya da takaicin da ya faru da mutane uku daga cikin wadanda   Hamasdin ke garkuwa da su,yadda bisa abun da suka kira kuskure,sojojin Isra,ilan suka bude musu wuta har lahira,a yayin da suka tunkarosu don su cecesu suna daga fararen tutoci da ke nuna alamun mika wuya