1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka da Isra'ila na duba yiwuwar kawo karshen yakin Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 18, 2023

Hamas ta ce hare-haren Isra'ila na Lahadin nan kan arewacin Gaza sun hallaka Falasdinawa 110.

https://p.dw.com/p/4aIkZ
Hoto: Nathan Howard/AP/picture alliance

Sakataren harkokin wajen Amurka Lloyd Austin ya sauka a Isra'ila a Litinin din, don tattauna batutuwan da ake kyautata zaton na dakatar da yakin Gaza ne, amma ta hanyar bin matakai daban-daban.

Wani babban jami'n tsaron Amurka ya shaida wa manema labarai da ke cikin tawagar sakataren tsaron na Amurka cewa Mr Austin zai gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da ministan tsaron kasar Yoav Gallant a yayin ziyarar.

Karin bayani:Za a ci gaba da kai kayan agaji a Gaza

A makon jiya ne mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro Mr Jake Sullivan ya kai ziyara Isra'ila, inda firaminista Benjamin Netanyahu ya shaida masa cewa zai ci gaba da yakin har sai ya kawar da duk wani burbushi na Hamas.

Karin bayani: Kasashen larabawa na yajin aiki kan Gaza

Kungiyar Hamas ta sanar a Litinin din nan cewa hare-haren da dakarun Isra'ila suka kai wa yankin arewacin Gaza a jiya Lahadi, sun hallaka Falasdinawa 110.

Ma'aikatar lafiyar yankin Gaza da ke karkashin ikon Hamas, ta ce a yankin Jabalia kadai an samu gawarwaki 50 a cikin gidaje.