1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gaza: Shugaban Hamas zai kai ziyara Masar

December 20, 2023

Shugaban Hamas zai kai ziyara kasar Masar domin bude sabuwar tattaunawa ta sake kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Falasdinu, biyo bayan amincewar da Isra'ilan ta yi don sake musayar fursunoni.

https://p.dw.com/p/4aN76
Hoto: AA/Stringer/picture alliance

Shugaban Hamas zai kai ziyara kasar Masar domin bude sabuwar tattaunawa ta sake kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Falasdinu, biyo bayan amincewar da Isra'ilan ta yi na sake tsagaita wutan domin musayar wasu fursunonin yaki.

Wannan ziyara na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya  ke ci gaba dsa kiraye-kirayen kawo karshen yakin, da  Majalisar Dinkin Duniya  za ta kada kura'ar amincewa da kawo karshen yakin baki daya.

Shugaban Hamas da ke zaune a Qatar Ismail Haniyeh, zai isa Alkahira tare da babbar tawaga, don bude kafar tsagaita bude wuta, kamar yadda wata majiya da ke da kusanci da kamfanin dillacin labarai na AFP ta shaida hakan.

A gefe guda, hukumomin Tel aviv na ci gaba da fuskantar matsin lamba na sakin fursunonin yakin Falasdinu da suka kama a yankin Gaza, da hukumomin suka ce a shirye suke su sake zama a teburin sulhu.

Shugaban kasar Israila Issac Herzog, ya ce a shirye su ke wajen tsagaita bude wuta domin sake gudanar da ayyukan jinkai, kamar yadda shima Firai ministan Isra'aila Benjamin Netanyahu, ya ce tuni ya tura wasu manyan jami'an leken asirin kasar zuwa turai wajen  samar da hanyoyin kubutar da 'yan Isra'ailan da ke hannun mayakan Hamas.