1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsara ficewar dakarun Faransa daga Nijar

October 7, 2023

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta sanar da cewa dakarun Faransa za su fice daga kasar a karshen wannan mako bisa tsauraran matakan tsaro karkashin rakkiyar sojojin kasar.

https://p.dw.com/p/4XEaE
An tsara ficewar dakarun Faransa daga NijarHoto: Dominique Faget/AFP

A cikin sanarwar da gwamnatin ta fidda ta ce an gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu domin tsara ficewar sojojin na Faransa da ke jibge a kasar inda aka cimma matsaya ta bai daya wacce ta shata ficewar illahirin dakarun kusan 1.500 kafin karshen wannan shekara.

Karin bayani: Faransa za ta janye sojojinta daga Nijar

Tuni ma dai aka kafa wata cibiya wace za ta lura da janye sojojin cikin aminci daga karshen wannan mako, farawa da dakaru 400 da ke jibge a Ouallam da ke yankin Tillabery na Yammacin kasar a kusa da iyakokin Mali da Burkina Faso.

Karin bayani: Sabon kawancen tsaro na Sahel zai fuskanci kalubale

A cikin wata sanarwa ta daban gwamnatin mulkin sojan ta ce ta aike ta wata tawagar i zuwa Ouallam domin wayar da kan al'umma kan halayar da za su nuna a lokacin ficewar sojojin don kadda a samu wata matsala.

Janye sojojin na Faransa dai na zuwa ne bayan takun saka tsakanin sojojin da suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum da Paris wacce tun da farko ta ce sojojin ba halastatun shugabanni ba ne kafin daga bisani ta karbi umurnin bayan matsin lamaba daga 'yan kasar ta hanyar zanga-zanga.

Karin bayani: Zanga-zangar korar sojijin Faransa a Nijar