1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta janye sojojinta daga Nijar

September 25, 2023

BAyan kwashe makonni ana takaddamar diflomasiyya tsakanin Faransa da Nijar, a karshe Shugaba Emmnuel Macron ya sanar da shirin janye sojojinsa daga Nijar.

https://p.dw.com/p/4WlKx
Sojojin Fanarsa a Nijar
Sojojin Fanarsa a NijarHoto: Dominique Faget/AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce kasarsa za ta kawo karshen dangantarkar soji a tsakaninta da Jamhuriyar Nijar.

Hakan na nufin Faransar za ta janye dakarunta 1,500 da ke a Nijar din nan da karshen wannan shekara.

Haka ma a cewar Shugaba Macron gwamnatin Faransa ta yanke shawarar mayar da jakadanta da ke a Nijar zuwa gida.

Kafin yanzun ma dai gwamnatin soja ta Nijar, ta bukaci jakadan na Faransa Sylvain Itte da ya fice daga kasar tun bayan juyin mulki na ranar 26 ga watan Yuli.

Sai dai duk da wa'adin sa'o'i 48 da Nijar ta debar wa jakadan a cikin watan jiya, jakadan bai fice ba.

Faransa dai ta ki amincewa da gwamnatin juyin mulkin da ke a Jamhuriyar ta Nijar.