1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawaye sun raba mutane da gidajensu

Salissou Boukari ZMA
July 13, 2023

A Jamhuriyar Nijar daruruwan mutane ne suka bar gidajensu jihar Tillabery, saboda barazanar hare-hare daga masu dauke da makammai a wannan yanki na iyakoki uku.

https://p.dw.com/p/4TrYy
Niger Diffa | Rückkehr von Flüchtlingen
'Yan gudun hijra Hoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Matsalar tsaro dai a yankin jihar Tillabery matsala ce da har yanzu take ci gaba da daukan hankali sosai inda a wannan lokaci na shigar damina inda mutanen karkara ke dukufa ga ayyukan noma, a wannan lokacin ne kuma su masu ikirarin jihadi da ke dauke da makammai a yankin ke tayar da zaune tsaye, inda ta kai har ma mutanen karamar hukumar Ouro Gueladjo da ke cikin gundumar Say cikin jihar ta Tillabery suka fuskanci barazana daga yan bindiga da suka bukaci da su fice su bar garuruwan ko kuma su fuskanci fushinsu.

Sai dai ganin cewa wannan yanki na a nisan yar tazara ne da yamai babban birnin kasar ta Nijar wasu da suka yi gudun hijirar sun zo har Yamai. Kaman yadda magajin garin Wuro Gelajo da shima ya zo Yamai ya yi tsokaci:

"Yankuna 17 ne aka nema da al'umma su fice su bar matsugunnansu, wadanan yankuna sun shafi manyan garuruwa hudu na karamar hukumar, A garin Wuron Geledjo iyallai 1171 ne suka bar garin wana adsadin jama'ar ya kai mutun dubu 10 da 808. A garin Toroid mun kidaya iyallai 327 wanda adadin jamar ya tashi 2,145 sannan a birnin Yamai kuma kidaya ta karshe da aka yi an samu mutun dari bakwai da 71 da suka gudo daga garuruwasnsu. "

Akasarin wadanda suka gujewa wannan tashin hankali na yan bidinga a yankin na gundumar Say, suns amu mafaka ne a wajejen yan uwa a nan unguwar bayan ruwa da ke nan birnin Yamai, sai dai kuma suna bukatar tallafi daga magabata tare da fatan ganin an dauki kwararan matakai da za su sanya su koma gidajensu.