1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maroko za ta karfafa kasuwanci da kasashen Sahel uku

Abdourahamane Hassane M. Ahiwa
December 28, 2023

Kasar Maroko ta bude kofofinta ga kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar, kasashen da ke fama da takunkumin karya tattalin arziki na ECOWAS. Kwanan nan Marokon ta shirya wani taro a Marrakech tare da wakilan kasashen.

https://p.dw.com/p/4afcw
Tashar jiragen ruwa a kasar Maroko
Tashar jiragen ruwa a kasar MarokoHoto: Walter G Arce Sr Grindstone Media Group/ASP Inc/Zoonar/picture alliance

Maroko dai tana son ba wa waɗannan ƙasashe damar shiga Tekun Atlantika domin yin fiton kayayyakinsu daga tekunta. Shin Marokon na neman samun tasiri a yanki na kafa huldar tattalin arziki a kasahen na Sahel.

Kusan faduwa ce ta zo daidai da zama ga kasashen na yankin Sahel, wadanda ba su dasawa da kungiyar ECOWAS. Maroko tana son yin amfani da wannan dama domin kara habaka tattalin arzikinta da kuma karfafa hulda tsakaninta da kasashen.

Akwai dai ayoyin tambaya a kan tayin da Marokon ta yi wa kasashen guda uku wanda ko daya daga cikin su, ba wanda yake da iyaka da kasar. Ko da an girka huldar ta kasuwancin tsakanin Marokon da kasashen na Mali da Nijar da Burkina Faso, dole ne kayayyakin da za su yi oda ta tashar jiragen ruwan Marokon, sai an ci kusan sama da kilomita dubu biyu kafin su kai gare su.

Ko kayan su biyo ta Aljeriya ko ta Mauritaniya kafin su isa Burkina Faso ko Mali ko Nijar, sabanin Benin da ke baki da hanci da Nijar da Burkina Faso wanda ya fi zama arha da sauki a gare su.  Ibrahima Kane, masani mai yin bincike a cibiyar  Open Society Initiative for West Africa (OSIWA) ya ce Marokon ta yi haka ne domin dama wa Aljeriya lissafi.

Guda daga cikin manyan kasuwanni a birnin Casablanca
Guda daga cikin manyan kasuwanni a birnin CasablancaHoto: Marco Simoncelli/DW

Masana dai na nazarin cewar wannan haɗin gwiwar da ake kokarin taso da shi, ta hanyar wannan shiri na samun damar shiga Tekun Atlantika, tsakanin Maroko da ƙasashen Sahel, shiri ne wanda ke da tsarin siyasa kawai.

Marokon na fafutukar kara samun karbuwa a yankin kasashen kudu da Hamada fiye da Aljeriya wacce da ma take yin takun saka da Maroko a kan batun Polisario da take goyon bayan masu neman 'yancin gashin kai don ballewa daga Marokon abin da ya dade yana bata wa Marokon rai. A wani bangaren ana tunanin cewar kasashen yankin yammacin Afirka sun tattauna da Marokon domin ta yi tayin ga kasashen na Sahel domin a hana su fadawa cikin hannun Rasha.

A dai halin da ake ciki har yanzu ko daya daga cikin kasashen uku ba wanda ya sanar da lokacin da zai fara huldar da Maroko domin yin amfanin da tashar jiragen ruwanta. Sannan ko da kasashen za su yi wannan hulda to kam idan har ba Marokon za ta yi musu wani rangwame na musamman, zai yi wuya a yi dan ci riba saboda nisan da ke tsakanin kasashen da bakin tekun na Maroko.