1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka tsakanin Maroko da Aljeriya

Mahamud Yaya Azare MNA
November 5, 2021

Watanni biyu bayan katse huldar diflomasiyya tsakaninsu, kasashen Aljeriya da Maroko na ci gaba da nunawa juna yatsa, lamarin da ke jawo fargabar barkewar yaki tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.

https://p.dw.com/p/42eHn
Kan iyaka tsakanin Maroko da Aljeriya
Kan iyaka tsakanin Maroko da AljeriyaHoto: Corentin Fohlen/maxppp/picture-alliance

Wani harin roka da ba a tantance daga inda ya bullo ba kan iyakar kasashen biyu da ya kai ga halaka sojojin Aljeriya uku, shi ne dalilin sabuwar dambaruwar tsakanin kasashen biyu, yadda Aljeriya ta fito karara ta tuhumi Maroko da kai harin cikin kasarta, tana mai shan alwashin daukar fansar da za ta sanya Maroko ba za ta sake tunanin akuyarta ta sake kusantar ramar kasar ta Aljeriya ba, inji Abdurrab Bin Sidrah, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Aljeriya.

"Wannan aika-aika ce da jirage masu tuka kansu na Maroko tare da hadin gwiwa da Isra'ila suka kai cikin kasar Aljeriya, har sojojinmu uku suka yi shahada. Ba za mu taba bari jininsu ya tafi a banza ba. Dole ne Maroko ta dandana kudarta nan ba da jimawa ba."

Tuni dai Maroko ta musanta wannan tuhumar, tana mai siffanta abin da ya faru da wani hatsarin taka nakiya da sojojin na Aljeriya suka yi a yankin da ake hana fararen hula kusantarsa saboda irin nakiyoyin da kasashen biyu da suka kwashe shekaru 30 suna rufe iyakokinsu da juna, biyo bayan yakin da suka gwabza.

Anwar Bu Zayeed, shi ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Maroko da ya ce:

"Muna da kwararan dalilan da ke tabbatar mana da cewa, batun cewa hari aka kai kan motar dakwan sojoji zuki ta malli ce. Ba ma kaunar yaki da makwabciyarmu Aljeriya. Ba za kuma mu taba yadda a tunzuramu shiga yaki da ita ba, duk kuwa da hakkin da muke da shi na kare kanmu. A madadin Aljeriya ta dinga zargin da ba shi da tushe, da kamata ya yi ta dukufa wajen magance matsalolinta na cikin gida da dakatar da goyan bayan da take bawa 'yan ta'addan Polisario da IS da kungiyoyin 'yan ta'adda na 'yan Shi'a 'yan barandan kasar Iran."

Karin bayani:Yamutsi tsakanin Aljeriya da Moroko

Irin wadannan zafafan kalaman da jami'an kasashen ke wa juna ya sanya wasu ke nuna fargabar kar kasashen biyu su sake tsunduma yaki a karo na biyu. Ko da yake Dr Siraj Sukhairaj, wani mai fashin baki dan kasar Aljeriya na tababa kan yiwuwar hakan, saboda matsalolin siyasa da na tattalin arzikin da Aljeriya ke fuskanta da kuma adawar da Amirka take da dagulewar lamura a yankin da zai iya ba wa Rasha da China kara samun gindin zama a cikinsa.

An jima ana samun takun saka tsakanin Aljeriya da Maroko, musamman saboda wani yanki da ke yammacin Sahara da Maroko ke kallo a matsayin mallakinta, amma Algeria ke goyon baya ga 'yan awaren yankin na Polisario masu fafatukar ballewa.

Alakar kasashen biyu ta dada lalacewa ne a 'yan kwanakin nan, har ta kai ga yanke hulda da dakatar da sayarwa Maroko iskar gas da Aljeriyan ke yi, sakamakon kulla alakar da Maroko ta yi da Isra'ila da kuma matakin ramawa kura aniyarta da Maroko ta dauka na goyan bayan kungiyar MAK ta yankin Kabylie mai neman 'yancin cin gashin kai daga Aljeriya.