1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jaridun Jamus: Yakin Sudan na kara ta'azzara

Usman Shehu Usman ZMA
November 17, 2023

Jaridun na Jamus a wannan makon sun dabu siyasar Laberiya da yakin Sudan da kuma yadda China ke ci gaba da mamaye kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/4Z5cL
Hoto: Pierre Honnorat/WFP/AP/picture alliance

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi magana kan George Weah, shugaban Laberiya mai ci da a yanzu haka ya yi fafatawar zaben zagáye na biyu, bayan da a zaben farko suka yi kunnen doki da babban abokin hammayarsa Joseph Boakai, wanda ke zama tsohon mataimakin shugaban kasa ne a kasar.

Don haka wannan zaben zagaye na biyu ne da ba shi da tabbas kasancewa a zaben farko kusan mutanen biyun babu wanda ya samu nasarar yawan kuri'un da ake bukata. Inda dukkaninsu dai ko wa ya samu sama da kashi 43 cikin dari.

Liberia | Präsidentschaftswahlen
Hoto: Rami Malek/AP Photo/picture alliance

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung ta duba yakin da ke kara kazanta ne a kasar Sudan. Jaridar ta ce barin wuta tsakanin sojan gwamnati da mayaka Khartum da Darfur na kara ta'azzara. Yunkurin sasanta bangarorin biyu da aka yi a birnin Jiddan Saudi Arabia bai kai ga tsagaita wuta ba. A cewar jaridar tun wancan lokacin ne fada ya kara kamari tsakanin bangarorin biyu.

Fada mafi muni a baya-bayan nan ya faru ne a Jebel Aulia da ke da nisan kilomita 45 daga Khartum babban birnin kasar, inda sojan gwamnati suka yi amfani da jiragen yaki, don jefa bama-bamai kan wuraren da mayaka suka ja daga. Mayakan RSF dai sun kara kama wurare da yawa musamman yammacin kasar, ind a yanzu kusan dukkan lardin Darfur ke karkashin ikonsu.

Sudan West Darfur | Geneina
Hoto: Str/AFP

Neue Zürscher Zeitung kuwa ta ce, a yanzu fa kasar China sai nausawa take cikin Afirka ta ko wane bangare ba kakkautawa. Jaridar na mai cewa kai hatta gidajen talabijin na Afirka sun koma yada farfagandar China. Sinawan dai na son kara samun karbuwa ga al'ummar Afirka da yanzu haka suke zuba jarin kudi a kasashensu. To amma fa jaridar ta ce yanzu kam harma an fara ganin wasu 'yan Afirka sun fara kosawa da 'yan China, inda ta bada misali da Kenya, kasar da aka ga masu zanga-zanga dauke da kwalayen da ke rubuce kuma suna rera wakar kyamar China.

Masu zanga-zanga a titunan Nairobi babban birnin kasar ta Kenya dai na cewa gaskiya sun gaji, kuma baza su iya yin goya 'yan kasuwar China wadanda ke samun komai da araha kuma, suna karya farashin kayayyaki, abin da ke sa ‘yan kasuwar Kenya sun kasa kaya bai cika basu riba kamar na yadda Sinawan ke samu ba. Wasu dai na ganin bayan Afirka ta kori turawan mulkin mallaka shekaru da yawa a baya, yanzu kuma sannu a hankali kasar China na neman maida Afirka mallakarta.