1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Laberiya a jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar SB/ATB
October 13, 2023

"Dimokuradiyya mafi tsufa a Afirka na neman hanyoyin fita daga cikin kunci da tashin hankali da cin hanci da rashawa" da haka jaridar Der Tagesspiegel ta bude labarinta kan zaben shugaban kasa da aka gudanar a Laberiya.

https://p.dw.com/p/4XVcz
Zaben Laberiya na shekara ta 2023
Zaben Laberiya na shekara ta 2023Hoto: John Wessels/AFP

Jaridar ta ce: Fiye da shekaru goma na yakin basasa da barkewar annobar cutar Covid-19 mai saurin yaduwa da kisa daura da 'yar uwarta ta Ebola, Laberiya na bukatar lokaci mai tsawo na daidaita lamuranta. Shugaba George Weah, dan wasan gaba na AC Milan da Chelsea, yana da burin zarcewa a kan shugabanci, yana neman wa'adi na biyu a kan karagar mulki a zaben da aka gudanar ranar Talata.

Zaben Laberiya na shekara ta 2023
Zaben Laberiya na shekara ta 2023Hoto: John Wessels/AFP

A cikin mawuyacin yanayi na rayuwar al'ummar ta Laberiya ne dai, inda cin hanci da rashawa da tsadar rayuwa ke damun al'umma aka gudanar da zabenb kasar acewar Andreas Schieder daya daga cikin wakilan tawagar EU da Austriya ta jagoranta a matsayin  hukumar sa ido kan zaben na Monrovia. Laberiya ba ta da girma, amma rashin kyawun ababen more rayuwa ya janyo kalubale wajen kai wa ga yankuna daban-daban. Ana daukar kasar dai a matsayin dimokuradiyya mafi tsufa a Afirka.

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung, sharhi ta yi a kan shafe watanni shida ana gwabza yaki a Sudan, inda ta ce akwai dalilai da suka sa yana da wahala a shimfida hanyar zaman lafiya a wannan rikici na manyan hafsoshin kasar guda biyu.

Jaridar ta cigaba da cewa tun a ranar 15 ga watan Afrilu wata tsawa mai tsanani ta girgiza Khartoum, babban birnin Sudan. Wannan dai ita ce rana ta farko da aka fara yakin da ake gwabzawa tsakanin wasu janar-janar biyu masu neman iko da kasar a kan kogin Nilu, kuma bayan watanni shida, har yanzu fafatawa da juna biyu.

Sudan | Janar  Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan da Mohamed Hamdan Dagalo
Janar Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan da Mohamed Hamdan DagaloHoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Rundunar Sojin kasa (SAF) ta na bin umurnin Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda ya yi juyin mulki, yayin da mayakan na Rapid Support Forces (RSF) wadanda rundunar sa kai ne ke mubayi'a Janar Mohamed Hamdan Daglo, wanda aka fi sani da Hemeti. Duk hafsoshin biyu na ganin za su samu nasarar warware rikicin, sai masu lura da lamuran siyasa na duniya na ganin cewar da wuya a gano bakin zaren warware rikicin da tuniya kashe dubban rayuka, daura da miliyoyi da suka kauracewa matsugunnensu, a yayin da wasu dubban ke gudun hijira a kasashe makwabta.

Bisa ga alamu EU na shirin fuskantar sabuwar barazanar a kasar Habasha, idan har ba a dauki matakai na hukunta wadanda suka aikata laifukan yaki ba a cewar jaridar Neue Zürcher Zeitung a labarinta kan irin barna da ayakin Tigray ya janyo a wannan kasa ta biyu mai yawan al'uumma a nahiyar Afirka.

Habasha, Addis Ababa | Jutta Urpilainen Kwamishinan Tarayyar Turai da Ahmed Shide ministan kudin Habasha
Jutta Urpilainen Kwamishinan Tarayyar Turai da Ahmed Shide ministan kudin HabashaHoto: European Union | CC BY 4.0

Jaridar ta ci gaba da cewar, lardin Tigray yana daya daga cikin yake-yake mafi muni da aka yi a shekarun baya-bayan nan. Sai dai kuma ya kasance wani rikici da mafi yawan al'ummar duniya ba ta lura da shi ba, rikicin da yayi sanadiyyar rayukan dubban daruruwan mutane tsakanin 2020 da 2022, a cikin tsaunukan arewacin Habasha.

Firayiminista Abiy Ahmed ya aike da sojojinsa zuwa can don ladabtar da mayakan tawaye da ke adawa da gwamnatinsa. Inda aka yi arangama tsakanin bangarorin biyu. Mutane sun mutu a fadace-fadacen, ta hanyar kisan kiyashi na fararen hula, yawancinsu saboda yunwa. A yayin rikicin an aiwatar da laifukan cin zarafin dan Adam ciki har da yi wa mata fyade ba gaira ba dalili. Wasu sun bayyana yakin a matsayin kisan kare dangi ne, kuma har yanzu ba a hukunta masu laifin ba.