1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jaridun Jamus: Yanayin Gaza ya ja hankalin jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 20, 2023

Fiye da mako guda da fara yaki tsakanin kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin Gaza na Falasdinu da sojojin Isra'ila, dubban mutane na dako a kan iyakar Masar haka ma motocin da ke dauke da kayan agaji

https://p.dw.com/p/4Xp7a
Gazastreifen | Trauer nach Raketeneinschlag | Ahli Arab Krankenhaus in Gaza
Hoto: Abed Khaled/AP/picture alliance

Dubban Falasdinawa sun kwashe kwanaki suna jira a kofar mashigar ta Rafah, kasancewar Isra'ila ta rufe dukkan hanyoyi biyu na Erez da Kerem da Falasdinawa za su iya bi domin shiga Masar. Mummunan harin da aka kai kan wani asibiti a yankin Zirin Gazan da ya halaka daruruwan mutane, ya kara dagula al'amura. Da yake ganawa da Shugaba Abdul-Fattah al-Sisi yayin ziyarar da ya kai birnin Al-Kahiran Masar, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bukaci a gaggauta bayar da damar kai kayan agaji yankin Zirin Gaza.

Mozambik | Hedikwatar Jam'iyyar RENAMO
Mozambik | Hedikwatar Jam'iyyar RENAMO Hoto: Bernardo Jaquete/DW

"Fargabar barkewar rikici, bayan babban zabe" in ji jaridar die tageszeitung. Jaridar ta ce akwai yiwuwar Mozambikta sake tsintar kanta cikin sabon rikicin siyasa, biyo bayan watsi da sakamakon zaben da aka gudanar a kasar a ranar 11 ga wannan watan na Oktoba wanda  jam'iyyar adawar kasar ta yi. Jaridar ta ce tun a ranar Talatar da ta gabata babbar jam'iyyar adawar Mosambik wato Renamo da ta kwashe tsawon shekaru 10 a matsayin kungiyar 'yan tawaye masu rike da makamai, ta yi kira da a ci gaba da zanga-zangar adawa.

Jam'iyyar Frelimo da ke mulki a kasar tun bayan da ta samu 'yancin cin gashin kai a shekarar 1975, ta lashe zabukan da aka gudanar a baki dayan yankuna 65 na kasar in ban da guda daya. Jam'iyar Renamo ta samu nasarar lashe zabe a birnin Beira mai tashar jiragen ruwa da ke da matukar muhimmanci ga Mozambik, yayin da jam'iyyar Frelimo mai mulki ta lashe zaben babban birnin kasar Maputo da kaso 58 cikin 100 kana Renamo ke da kaso 33 cikin 100 kacal.

Rikicin Sudan
Rikicin SudanHoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Bari mu karkare da jaridar Neue Zürcher Zeitung a sharhinta mai taken: Maganar gaskiya? Ba ni da sauran fata." Jaridar ta ce wakiliyar musamman ta kungiyar Tarayyar Turai EU a yankin Kahon Afirka, na ganin babu ranar kawo karshen yakin basasar da ake fama da shi a Sudan. Yaki ya barke a kasar tun cikin watan Afrilu tsakanin sojojin kasar karkashin jagorancin Shugaba Abdelfatah al-Burhan da kuma jagoran kungiyar tawayen RSF Mohammed Hamdan Daglo.

Babban birnin kasar Khartoum da kimanin mutane miliyan bakwai ke zaune a cikinsa gabanin yakin, na fuskantar hare-haren bama-bamai. An rufe makarantu a yankunan kasar da dama, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa an gano tarin manyan kaburbura da aka binne mutane a Darfur. Sama da mutane miliyan hudu na gudun hijira, yayin da dubbai suka halaka. Duk kokarin al'ummomin kasa da kasa na shiga tsakanin, ya gaza yin tasiri mai yawa.