1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Faransa za ta alkawarta tallafawa ECOWAS kan Dimokradiyya

November 3, 2023

Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ce ta bayyana hakan a juma'ar nan a Najeriya

https://p.dw.com/p/4YOFi
Hoto: Francis Kokoroko/REUTERS

Faransa ta alkawarta tallafawa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, wajen ganin mayar da yankin kan turbar Dimokradiyya tsantsa, biyo bayan yadda sojoji ke hambarar da wasu gwamnatocin siyasar yankin Sahel.

Karin bayani:ECOWAS za ta dawo da dimukuradiyya a Nijar

Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ce ta bayyana hakan yau juma'a a Najeriya, yayin wata ziyarar aiki don tattauna batutuwan da suka shafi harkokin tsaro, don ganin an mayar da kasashen Mali Burkina Faso da kuma Nijar kan mulkin Dimokradiyya, bayan sojoji sun kwace mulki da karfin bindiga.

Karin bayani:ECOWAS: Wanne mataki za a dauka a Nijar?

ECOWAS dai ta kakabawa Jamhuriyar Nijar takunkumin karya tattalin arziki tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum, tare da tsare shi da iyalansa.