1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS za ta dawo da dimukuradiyya a Nijar

September 20, 2023

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce yana neman hanyoyin warware rikicin siyasa da Jamhuriyar Nijar ta fada a ciki, bayan juyin mulki da aka yi a kasar cikin watan Yuli.

https://p.dw.com/p/4WaAw
Shugaban Najeriya | Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola TinubuHoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

Shugaba Bola Tinubun da ke fadin haka ranar Talata, ya ce yana marhabin da duk wata shawara ko tallafin da za su kai ga dawo da Nijar bisa tsari na dimukuradiyya.

Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS mai kai komon ganin ta maganta rikicin na Nijar, tun da fari ya yi barazanar amfani da karfin soji muddin dai hanyoyin lalama na diflomasiyya suka gaza wani katabus.

Cikin jawabinsa a birnin New York, shugaban na Najeriya ya wofinta juye-juyen mulkida ke kama da yayi a wasu kasashen yammacin Afirka a shekarun baya-bayan nan.

Tinubun ya kuma ce suna dai tattaunawa da jabanannin sojojin na juyin mulki lokaci zuwa lokaci.