1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Makomar matakin ECOWAS ko CEDEAO

August 8, 2023

Shugaban Najeriya Bola Ahmand Tinubu da ke jagorantar kungiyar Ecowas, ya nuna bukatar amfani da diflomasiyya maimakon amfani da karfin soji wajen warware rikicin shugabncin Nijar.

https://p.dw.com/p/4UvaR
Najeriya | Abuja | ECOWAS | CEDEAo | Taro | Nijar | Juyin Mulki
Shugaban Najeriya kana jagoran ECOWAS ko CEDEAO, Bola Ahmed TinubuHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Wannan halin ko-in-kula da sojojin da suka kifar da gwamnati a Nijar din ke nunawa, na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ke nazarin mataki na gaba kan sojojin in har suka ki mayar da mulki ga hambararren shugaban kasar Muhammed Bazoum. Birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya na shirin sake karbar bakuncin kasashe da wakilai mambobin kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO, domin fitar da matsaya kan masu kwacen mulkin na Nijar. Sai dai suma sojojin sun fitar da matakai da ba su yiwa ECOWAS ko CEDEAO din dadi ba, kama daga batun rufe iyakokin kasar da kuma hana jiragen sama shawagi a sararin samaniyar kasar.

Karin Bayani: Nijar: Makomar sojojin Jamus a Sahel

Mai magana da yawun sojojin Amadu Abdurrahmane ya bayyana matakan a wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin, inda ya ce duk jirgin da ya keta sararin samaniyar kasarsu to babu shakka zai fuskanci hukunci mai tsanani. Idan ka kalli taswirar Jamhuriyar Nijar din dai, ta yi fadin kasar Faransa har sau biyu da dole ne dukkan jiragen da ke zirga-zirga tsakanin kasashen duniya da nahiyar Afrika su keta ta sararin samaniyarta. Tuni dai jirgin Air France ya katse zirga-zirgarsa tsakanin birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso da Bamako na kasar Mali, kasancewar dukkanninsu sun yi iyaka da Nijar din. Tsohon shugaban Hukumar Inshora ta Najeriya kuma mai sharhi kan alamuran yau da kullum Farfesa Usman Yusuf ya ce, akwai sarkakiya wajen daukar matakin soja kan Nijar din  yana mai cewa bin hanyar diflomasiyya ne masalaha.

Najeriya | Abuja | ECOWAS | CEDEAo | Taro | Nijar | Juyin Mulki
Jagoran gwamnatin juyin mulkin sojan Nijar, Abdourahmane Tchiani Hoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Ga dukkan alamu dai ECOWAS ko CEDEAO za ta tashi gwiwarta a sanyaye, sakamakon matsin lambar da take fuskanta daga cikin kungiyar da nahiyar har ma daga kasashen duniya. Ga misali kasar Aljeriya da ta yi iyaka da Nijar ta ce kai wa Nijar hari kamar kai wa arewacin kasarta farmaki ne, inda Shugaba Abdulmajid Tabboune ya bukaci a yi amfani da diflomasiyya. A yayin da ECOWAS ke nazari kan martanin da sojojin Nijar din za su mayar da kuma kiraye-kiraye daga kasashe kamar Aljeriya, kwatsam sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya ce Whitehouse na cike da burin ganin an warware matsalar ta hanyar amfani da diflomasiyya kamar yadda ya bayyana a kafar yada labaran Faransa ta RFI.

Karin Bayani: 'Yan siyasar Nijar sun ce sai an dawo da Bazoum

Farfesa Usman ya ce ba wai gayawa gwamnatin Tinubu ta yi ba ko kuma kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, kawai abin da ya kamata a yi shi ne bijiro da tsare-tsaren da zai kai ga warware takaddamar ta hanyar amfani da dukkanin daftarin diflomasiyya. Farfesan dai, ya kara da yin tir da daukar matakin sanya takunkumi ga Nijar saboda juyin mulkin. Ta tabbata dai ECOWAS ko CEDEAO da a baya ta kasance abin kwatance a idanun duniya, na fuskantar barazana mafi girma ta dusashewa. Gwamnatocin mulkin soja a kasashen Mali da Burkina Faso sun nuna goyon bayansu ga sojojin Nijar, kamar yadda kakakin sojan Mali Abdullaye Maiga ya nunar. A cewarsa suna tare da Jamhuriyar Nijar dubu bisa dubu, kuma dakarun Nijar za su yi nasara a wannan gwagwarmaya a jawabin da ya gabatar da yawun shugaban kasar Kanal Asimi Goita.